✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kula da kafa lokacin sanyi

Ga hanyoyin da zaku bi don kare kanku daga lalacewar kafa lokacin sanyi.

Kafa tana daya daga cikin gabban da suka kamata mu kula da su. Domin idan ba a kula da kafa ba, hakan na iya janyo kauje ko faso.

A rage dadewa a cikin ruwa idan an zo wanka. Yana da kyau a rika wanke tafin kafa da ruwan dumi ba tafasasshe ba.

Sannan yana da kyau ana shafa mai a kafa a duk lokacin da tafin kafar ya gamu da ruwa. Sa’annan a rage sanya takalma wadanda iska ba zai samu kafar ba.

  • A tsoma tafin kafa a ruwan lemun tsami na tsawon minti 10. Yin hakan na fitar da matattun fata daga tafin kafa. Sannan a samu dutsen goge kafa a dirza ta.
  • Za a iya hada man tafin kafa idan aka hada man zaitun da ruwan lemun tsami sai a rika shafawa a inda ta tsage. Ana girgiza wannan hadin kafin a yi amfani da shi a kullum.
  • A rika shafa man basilin a tafin kafa, sannan a sa safa a kullum kan a kwanta barci.
  • Kashi uku bisa hudu na kofin man kwakwa da rabin na man kadanya na gyara tafin kafa. Idan aka samo su sai a hada su sannan a narkar da su a wuta. Bayan sun narke, sai a shafa a tafin kafa sannan a sanya safa kafin a kwanta.
  • Kada a tsoma kafa a ruwa salam haka, ba tare da an yi wa ruwan wani hadi da abubuwan da na lissafa ba.
  • A rika shafa mai kafin a kwanta barci, sannan a sa safar kafa.