✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za a kula da lafiyar fata a lokacin sanyi

Hanyoyin da za a bi domin kare lafiyar fatar jiki a lokacin sanyi.

Idan aka fara jin iska mai kura da hazo tana kadawa, to da alama lokacin sanyi ya zo.

Wasu suna yawan korafi a kan yanayin sanyi, amma ga wasu, yanayi ne mai da dadi, musamman idan mutum na kwance a lullube, iska mai na kadawa, sai mutum ya ji kamar kar ka sauka daga kan gado.

Lokacin sanyi yana farawa ne daga watan Nuwamba zuwa Maris, kuma a lokacin fata da leben mutane na bushewa.

Akwai abubuwa da ya kamata mu rika yi don kula da lafiyarmu a lokacin sanyi.

A lokacin sanyi mutum na bukatar kayan sanyi kama rigar sanyi, safa, dogon wando da riga mai dogon hannu da lulluba da bargo idan za a yi barci.

A rika amfani da man shafawa da zai dade a jiki kamar man zaitun, basilin, ko man kwakwa bayan an yi wanka domin kada fata ta yi fari.

Sannan a rika shafa man a lebe saboda a lokacin sanyi fata tana bushewa da wuri.

A dinga sha ruwa ko madara ko shayi saboda jikinmu dan Adam na bukatar ruwa sosai, domin ruwa na taimaka wa jini gudana a jiki.

A lokaci sanyi iska tana tashi da kura wanda ke iya sa mutum ya kamu da cututtukan kamar mura, tari da ciwon huhu.

Don haka mutumin da yake da cutar asma bai kamata ya dinga yawo ba tare da abin rufe fuska da kuma inhaler sa ba.