Yadda za a magance barazanar tsaro da ta’addanci a Najeriya — Buratai | Aminiya

Yadda za a magance barazanar tsaro da ta’addanci a Najeriya — Buratai

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya
Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya
    Bashir Yahuza Malumfashi

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyyar Benin, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya ce matukar ana so a magance barazanar tsaro da ayyukan ta’addanci da suke addabar sassan Najeriya, tilas ne a magance matsalar tun daga tushe, musamman ta hanyar bincike da daukar kwararan matakan tsaro.

Jakadan ya fadi haka ne a ranar Juma’ar makon jiya, yayin gabatar da wata lacca, a wurin bikin yaye dalibai karo na 24 da 25 da 26 na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola a Jihar Adamawa.

Ya ce babu wata kasa da za ta iya magance barazana da ayyukan ta’addanci sai ta koma tun daga tushe ta kashe jijiyoyin da suka haifar da ta’adanncin.

“Ya zama dole a samar da ingantacciyar gwamnati mai inganta rayuwar al’umma.

“Kuma sai an karfafa cibiyoyi da ma’aikatun gwamnati, domin su rika aikin al’umma yadda ya dace, sannan a samar da tsaro a yankunan da suke fayau, ta hanyar kai musu jami’an tsaro da samar masu da ayyukan yi da sana’o’i.

“Sai an magance karuwar talauci, wadda take samuwa a sanadiyyar zaman kashe wando da matasa ke yi.

“Sannan a bunkasa rayuwar mazauna karkara, ta hanyar samar masu da kayayyakin inganta rayuwa.”

Duk wannan dai na zuwa ne a laccar da ya gabatar mai taken: “Dakarun Najeriya a Fagen Yaki da Ta’addanci: Samar da Tsaro ko Bunkasa Kasa?”

Janar Buratai ya bayyana dalilinsa na gabatar da wannan lacca, wacce ya ce an shirya gabatar da ita tun yana kan shugabancin Rundunar Sojin Najeriya, a bara amma saboda dalilin cutar Coronavirus da ta addabi duniya, aka dage bikin har sai wannan lokaci.

Ya ce daga wancan lokaci zuwa yau, babu shakka an samu ci gaba wajen yaki da ’yan ta’adda a kasar nan.

Ya kara cewa wannan nasara tana samuwa ne sakamakon yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake ba wa sojoji da sauran jami’an tsaro kyakkyawar gudunmawa, ta hanyar inganta su da kayan aiki da sauransu.

Janar Buratai, wanda aka karrama kuma shi ne Babban Babo Mai jawabi a wurin bikin, ya ce abin da ake yi yanzu na gudanar da harkokin tsaro yana tafiya daidai saboda irin gudunmawar da Shugaba Buhari yake bayarwa a wajen tsaretsaren da ake yi.

“Wannan ya kara tabbatar da nasarar da aka samu kan ’yan Boko Haram.

“Yadda ake gina Arewa maso Gabas shi ne babban jigon samun nasarar tabbatar da tsaro a yankin baki daya,” inji shi.

Ya ce irin yadda aka tagayyara ’yan ta’addar Boko Haram da danginsu ’yan Ansaru da ISWAP a Arewa maso Gabas da yankin Tafkin Chadi, abin ya yi tasiri matuka.

Sai dai ya ce har yanzu suna da dan karsashin kai harehare nan da can, musamman wuraren da suke mazaunan raunanan mutane ne.

Ya ce don haka wannan babban kalubale ne ga gwamnati da dakarunta su kara kaimi don ganin an samu cikakkiyar nasarar yaki da ’yan ta’adda.

“Domin ganin an samu cikakkiyar nasara, wajibi ne a mai da hankali wajen samar da tsauraran matakan tsaro da gudanar da mulkin adalci da sasanci da yin sulhu da ’yan ta’addar da suka nuna sha’awar tuba na gaskiya.

“Haka kuma a inganta jin dadin al’umma, musamman ta samar da ababen more rayuwa a karkara da sauransu,” inji shi.

Babban bako mai jawabin, ya ce: “Ina da masaniyar matsalolin da suke tattare da yakin da ake da ta’addanci, musamman a matsayina na tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya da kasancewata Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin a yanzu, wadannan matsayi sun ba ni damar sanin abin da zan fada dangane da matsalolin tsaro.

“A yanzu ina da tabbaci da masaniyar cewa amfani da karfi wajen tunkarar ’yan ta’adda abu ne mai kyau, sai dai kuma ya zama wajibi mu fahimci cewa aikin ba na sojoji ba ne su kadai kuma aikin ba na karfi ba ne kadai, sai an hada da wasu matakai da sauran hikimomi da dabaru.”

Janar Buratai ya kawo faffadar ma’anar ta’addanci a cikin laccar tasa, inda ya ce wani tsari ne da wadansu suka kitsa domin cim ma wata manufa ta siyasa, kuma ya ce babu wani dan ta’adda da yake na’am da a kira shi da wannan suna.

“Wani dalili da ya sa ta’addanci bai da tsayayiyyar ma’ana shi ne, saboda an tanadar da shi ne saboda cim ma wata manufa ta siyasa kuma suna ne da ke da mummunar ma’ana.

“Ni dai ban san wata kungiya da take murna a lakaba mata wannan suna ba, ko da kuwa aikin da take yi na ta’addancin ne,” inji masanin tsaron.

Ya ce ta’addanci wani aika-aika ne da wani mutum ko kungiya ke aiwatarwa a kai-akai, wanda ya hada da cin zarafi, da saka tsoro da firgici da kashekashe da lalata dukiya ko kwace da sauransu a kan wata al’umma ko yanki domin cim ma wata bakar manufa ta siyasa ko ta laifi da niyyar aika wani ayyanannen sako ga wadanda aka nufa.

‘Dalilin da ake yi wa gwamnati tawaye’

Da ya juya kan kalmar tawaye, ya ce wannan tana nufin wani yunkuri ne na daukar makamai da ake yi a kan wata gwamnati ko yanki da nufin amshe ikon tafiyar da gwamnatin ko ikon gudanar da harkokin yau da kullum da tasarrafin dukiyar yankin.

Wata kungiya mai ra’ayin siyasa ko addini ko al’ada ko bangaranci ke aiwatar da irin wannan aikaaika bisa ayyananniyar manufar da ta kitsa wa kanta.

Janar Buratai ya bayyana hikimomi da dubarun da ake dauka domin magance ta’addanci da ’yan ta’adda, wadanda ya ce sun hada da amfani da karfin soja da karfin ikon gwamnati.

Kuma ya ce sai an hada da hikimar diflomasiyya da fadakarwa da amfani da dukiya.

Ya ce idan aka samu wanzuwar wadannan al’amura, akwai yiwuwar a samu cikakkiyar nasarar dakile ta’addanci.

Ya kara da cewa, hanyoyin da za a bi a dakile tawaye da ’yan tawayen su ne “ya zama dole an hada karfi da karfe a tsakanin soji da sauran jami’an tsaro da wasu hanyoyi na daban, wadanda suka hada da matakin shari’a da tattalin arziki da kuma hikimomin rarrashi da lallami.”

‘Mu rika daukar izina’

Janar Buratai ya ce idan gemun dan uwanka ya kama wuta sai ka shafa wa naka ruwa, kuma bisa ga haka, ya ce domin yaki da ta’addanci da tawaye, ya zama wajibi Najeriya ta dauki darasi daga wasu kasashen duniya da suke fuskanta ko suka taba fuskantar kalubalen tsaro da ta’addanci.

Ya ba da misali da kasar Sirilanka da Somaliya da Kolombiya, inda ya ce dukkan wadannan kasashe sun dauki matakai da dabaru iri-iri, wajen ganin sun magance barazanar tsaro daga ’yan ta’adda da ’yan tawaye.

Ya ce lallai ne a yi nazarin matakai da hanyoyin da kasashen Sirilanka da Kolombiya suka dauka a yaki da ta’addanci, domin a yi koyi da su.

Ya ce wadannan kasashe biyu sun samu nasara, a yayin da Somaliya ta gaza samun nasara.

Duk da haka, ya ce abu ne mai amfani Najeriya ta dubi dalilin da ya sanya Somaliya ta gaza, yayin da sauran biyun suka yi nasara.

A cewarsa, koyon darasi daga wanda ya gaza ma abu ne mai amfani domin kiyayewa.

Daga karshe, Janar Buratai ya nanata hanyoyi mafiya dacewa wajen magance ayyukan ta’addanci da tawaye.

“A ra’ayina samar da tsaro da bunkasa kasa a Arewa maso Gabas abu biyu ne da bai kamata a rarrabe su ba, sai dai a dauke su a matsayin mas’ala daya, domin kuwa matakan bunkasa kasa abubuwa ne da ake tsananin bukata domin daidaita al’amura da magance matsalar tsaro.

“A yayin da ake tunkarar ’yan Boko Haram da karfin soja, ya zama wajibi mu duba musabbaban da suka haddasa shigar su ayyukan ta’addanci.

“Ke nan, za a yi nazari na musamman, a fito da hikimomi da dabarun samar da tsaro da bunkasa kasa, a matsayin sahihan matakan magance matsalolin ta’addanci da tawaye a Najeriya,” inji shi.