✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance rashawa a Najeriya — Shugaban Media Trust

Ya zama tilas mu rika saka wa nagarta da kwazo a wuraren aiki.

Shugaban Majalisar Daraktocin Kamfanin Media Trust Limited, masu buga jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Kabiru Yusuf, ya ce dole ne ma’aikatu da kamfanoni a Najeriya su rungumi al’adar ba da kyautuka kan kwazo da nagartar aiki domin yakar cin hanci da rashawa.

Kwararren dan jaridar ya bayyana hakan ne a daren jiya na Laraba yayin da kamfanin ke gudanar da bikin karrama ma’aikatan da suka nuna nagarta da dadewa a aiki karo na 11 a babban ofishin kamfanin da ke Abuja.

A cewar Mallam Yusuf wanda ke zaman Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Jarida ta Najeriya, NPAN, bayar da ladar ingancin aiki ga ma’aikaci na daga cikin hanyoyin magance rashawa a kasar nan.

Ya yi watsi da ikirarin a wadansu ke yi cewa Kamfanin yana nuna bangaranci, inda ya jaddada cewa kyaututtukan da aka gabatar sun nuna cewa babu batun kabilanci yayin zabo wadanda aka karrama.

“Kowa yana magana game da cin hanci da rashawa a Najeriya, shin ta ya za mu kawar da wannan matsala

“Dole ne mu rika saka wa nagarta kuma abin da muke kokarin yi ke nan a nan.

“Abin da muke nufi shi ne idan ka yi aikinka da kyau kuma ka kare abin da muka mallaka gaba dayanmu, to ba za mu manta da kai ba.

“Za mu dore da yin hakan domin kara daga likkafar Kamfanin gaba.

“Kamar yadda ka sani, Kamfanin shi ma yana fuskantar radadin annobar COVID-19 wanda abu ne da ya zama ruwan dare gama duniya. 

“Akwai durkushewar tattalin arziki ga matsalar tsaro, sai dai mu a nan, muna yunkurawa wajen yin abin da ya dace mu yi.

“Duk wanda ya yi himma muna saka masa sannan ba ma duba fuskokinsu face muna duba kwazonsu ne,” inji Shugaban.

Ya kuma bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen kafa Gidan Talabijin kari kan jaridun Daily Trust da Aminiya.

Sannan ya shawarci ma’aikatan da su zama masu da’a ga ka’idojin aikin kamfanin, yana mai cewa idan aka kammala aikin Gidan Talabijin din zai dafa wa ayyukan da jaridun Kamfanin ke gudanar wa.

Ma’aikata 41 ne kamfanin ya karrama da lambobin yabo daban daban ciki har da kyaututtukan kudi.