✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance rashin tsaro a Najeriya

Babban Limamin Cocin Katolika da ke birnin Abuja, Ignatius Kaigama, ya shawarci gwamnatin jihohi da tarayya da sauran masu ruwa da tsaki, da su sauya…

Babban Limamin Cocin Katolika da ke birnin Abuja, Ignatius Kaigama, ya shawarci gwamnatin jihohi da tarayya da sauran masu ruwa da tsaki, da su sauya salon tunkarar kalubalen rashin tsaro da ya addabi kasar.

Kaigama ya nemi dukkan masu ruwa da tsaki, da su kara zage dantse wajen kawo karshen kashe-kashe da zubar jinin al’umma da suka zamto ruwan dare a fadin tarayyar.

Jagoran mabiya addinin Kiristan ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis, yayin amsa tambayoyin manema labarai bayan taron daga likafarsa a cikin jerin sahun Limaman addinin a Najeriya.

A cewarsa, muddin gwamnatin da sauran hukumomin tsaro suka yi tsayuwar daka a kan kashe-kashe, garkuwa da mutane da ta’addancin ’yan faahin daji da suka addabi wasu sassan kasar, to kuwa cikin kankanin lokaci lamarin zai zamto tarihi.

Ya nemi mahukunta na kasar a kowane mataki da suka fifita samar wa ’yan Najeriya tafarkin tsira fiye da komai.

Ya kuma bayyana takaici a kan yadda a mafi akasarin lokuta hankoron madafar iko yake mamaye duk wani yakin neman zabe a madadin bayar da muhimmanci a kan yadda za a kawo sauki na rayuwa ga talakawan kasar.