✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance warin hammata

Man amfuna na taimakawa wajen magance warin hammata.

Akwai abubuwa da dama da suke haifar da warin hammata musamman a lokacin zafi.

Yawan sa kaya matsattsu ko kaya sau biyu a lokacin zafi kan haifar da warin hammata.

Idan kuma mutum mai yawan shan giya ce, ba wuya ya rika yin warin hammata.

Don haka a yau na kawo muku hanyoyi da za a bi domin rabuwa da warin.

• A samu lemun tsami a raba biyu a goga a hammata bayan an yi wanka.

Ko kuma a matse ruwan a samu tawul a rika tsomawa ana shafawa a hammata bayan an yi wanka kafin a sa riga, yin haka na magance wannan matsala.

• Rose water na taimakawa wajen magance warin hammata.

Don haka a rika diga ruwan a ruwan wanka kuma a shafa a hammata bayan an yi wanka.

• A matse ruwan tumatir sannan a shafa a hammata na tsawon minti 15, sannan a shiga wanka.

Amma irin wannan zai dan dauki lokaci kamar mako daya kafin a rabu da warin hammatan.

• Amfani da alimun na taimakawa matuka; a tsoma alimun a ruwa sannan a shafa ruwan a hammata sannan a bar ruwan ya bushe. Yin haka na magance warin hammata.

• Hodar jarirai na magance warin hammata domin suna dauke da kamshi sai a rika shafawa a hammata a kullum bayan an fito wanka.

• An san itacen ‘Sandalwood’ da kamshi sai a samu hodarsa a kwaba da ruwa sannan a shafa a hammata na tsawon minti 20 sannan a wanke.

• Man amfuna na taimakawa wajen magance warin hammata. A samu man amfuna a shafa a hammata bayan an fito wanka.