✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a samu fatar fuska mai sulbi

Hanyoyi biyar na kawar da kuraje da kuma hana fesowarsu a fuska.

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na kwalliya.

Kamar yadda ake cewa “riga-kafi ya fi magani” don haka ne a yau na kawo muku hanyoyi biyar da za a bi domin kare fuska daga fesowar kuraje da wasu cututtuka.

Yana da kyau mace ta fi kulawa da fuskarta fiye da komai a jikinta. Domin, kafin a hango komai a jikinta, fuskar za a fara hangowa.

  • Ana iya yi wa fuska tausa.

Kamar yadda kowace gaba a jiki ke son tausa, haka fuska ma tana son ana yawan yi mata tausa kamar sau daya a rana.

Yin tausa ga fuska na taimakawa wajen kara karfin fuska da kuma kare ta daga yankwanewa da wuri a lokacin tsufa.

  • A kasance ana yawaita wanke hannu.

Domin hannu na dauke da wasu cututtuka da idanu ba su gani. Ya kamata ana wanke hannu sosai a kullum kafin a wanke fuska da shi ko kuma a shafa mata man fuska.

Idan hannu mai dauda ya hadu da fuska, hakan zai haifar da wasu kwayoyin cuta a fuskar.

  • Kafin a shafa wani mai a fuska, yana da kyau a bude ramukan gumi a fata.

Kuma hakan zai yiwu idan ana wanke fuskar da ruwan dumi, ko a saka tawul a ruwan zafi sai a goge fuskar da ita sannan a shafa man.

Yin haka na taimaka wa man fuska aiki sosai ba tare da bata lokaci ba.

  • Yana da kyau kafin a wanke fuska a goge ta da magogin fuska.

Yin haka na fitar da matacciyar fata da ta daskare a fuska. Bayan haka sai a wanke ta.

Magogin fuska daban yake da magogin hakori, don haka, za a iya samun magogin fuska a manyan kantunan da suke sayar da kayan kwalliya.

  • Sannan kada a sake a yi wasa da cin abinci mai dauke da sinadarin ‘calcium’ kuma a rika shan maganin da zai kara wa kashinmu karfi.

Yawan shan ‘calcium’ zai hana fuska fita daga kamanninta na da koda an tsufa.