✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ku ribaci kwanaki 10 na farkon watan Zhul-Hijjah

Bayanin abubuwan da Musulmi zai yi domin cin ribar ranaku mafiya alheri a shekara.

A yayin da Zhul-Hijjah ke dab da kamawa, malaman addinin Musulunci na ci gaba da kira ga al’umma kan yadda za su ribaci falalar kwanakin kwanaki 10 na farkon watan yadda ya kamata.

A tattaunawarsa da Aminiya, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Triumph da ke Kano, Shaikh Lawal Abubakar ya ce kwanakin na da matukar falala ta Allah Madaukakin Sarki Ya yi rantsuwa da su a Alkur’ani.

Ya ce “Kwanaki ne mafiya cikin watanni masu alfarma. Manzo (SAW) ya ce ba wani aikin alheri da mutum zai yi a tsawon shekara da Allah Ya fi so sama da a wadannan kwanakin, saboda haka ake so Musulmi su yawaita ibadu a cikinsu”.

Abubuwan da ake so mutum ya yi a kwanaki goman Zhul-Hajj

“A wadannan kwanaki, ana so mutum ya yawaita salati, istigfari, hailala, salatin Annabi (SAW), karatun Kur’ani, nafiloli har ma da azumi.

“Ana kuma so Musulmi ya yawaita sadar da zumunci da bayar da sadaka a wadannan kwanakin.

“Ana so mutum ya azumci wadannan kwanakin guda goma, sai dai ga wanda zai yi aikin Hajji ba zai azumci ranar Arfa ba.

“Ga wanda kuma ba zai je aikin ba shi ma ma ba zai azumci ranar cikon ta goman ba, wacce ita ce ranar Sallah saboda an hana azumi ranar Sallah.

“Ko da mutum ba zai samu damar azumtar kwanakin ba ana so kada mutum ya yi akalla na tara ga watan nan (ranar Arfa) saboda shi ne ya fi sauran falala (ga wanda bai je aikin Hajji ba), inji shi.

Mai halin yin layya

Kazalika, malamin ya shawarci Musulman da ke da ikon yin layya da kada su yanke faratansu ko kuma su yi aski a ciki wadannan kwanakin kamar yadda Sunnah ta koyar.

Yawaita sadaka

Shi ma Malamin Musuluncin kuma shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Shaikh Ibrahim Khalil ya ce ibadar da aka fi so Musulmi ya yi a kwanakin ita ce sadaka.

Ya ce, “Ya kamata Musulmai su dage wajen bayar da sadaka ko ta abinci ko wani abun saboda ita ce nau’in ibada mafi soyuwa a wadannan kwanakin.

“Sannan sai azumi sai nafiloli, karatun Alkur’ani da kuma zikiri.

Yi wa kai hisabi

Shaihin malamin ya kuma ce ana bukatar Musulmai su yi amfani da kwanakin wajen yi wa kansu hisabin shekarar.

“Musulmi ya yi wa kansa hisabi ta hanyar tambayar kansa me ya yi tun daga farkon watan Muharram har zuwa yanzu?

“Mene ne ya yi ba daidai ba me kuma zai yi ya gyara a shekara mai zuwa?”, inji Shaikh Ibrahim.

Malamin ya kuma shawarci Musulmi da su dage wajen yawaita addu’o’i musamma a ranar Arfa (tara ga wata) saboda babu ranakun da Allah Yake amsa addu’o’i sama da wadannan.