✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ku yi rajistar katin shaidar zama dan kasa

Sama da mutum miliyan 42 sun yi rajistar shaidar zama dan kasa a Najeriya

Najeriya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen bikin Ranar Shaidar Zama Dan Kasa ta 2020, a ranar 16 ga watan Satumba.

Hukumar da ke Kula da Shaidar Zama Dan Kasa a Najeriya (NIMC) ta ce akalla ‘yan kasar miliyan 42 ne suka yi rajistar katin zama dan kasa.

To sai dai mutane da dama na ganin adadin ya yi kadan idan aka yi la’akari da yawan mutanen da kasar da ya haura mutum miliyan 200.

Ana bikin Ranar Shaidar Zama Dan Kasa ce domin wayar da kan jama’a kan bukatar samun shaida ga dukkanin al’ummar duniya.

Rahotanni sun nuna akwai mutum sama da biliyan daya da har yanzu ba su da cikakkiyar shaida a hukumance, kuma kusan kaso 81 daga cikinsu sun fito ne daga yankin Afirka kudu da hamadar Sahara da kuma Kudancin nahiyar Asiya.

Ga kadan daga cikin matakan da za ku bi domin mallakar katin shaidar zama dan kasa a Najeriya.

  1. Ga dukkan mai sha’awar yin katin zai ziyarci shafin NIMC da ke https://penrol.nimc.gov.ng/loginForm.tpl.html.php domin cike muhimman bayanansa kamar suna, adireshin imel da kuma lambar tsaro ta sirri.
  2. Daga nan in an kammala sai a fitar da takardar shaidar kammalawa a ziyarci ofishin da NIMC ta tanadar domin kammala yin rajistar.
  3. Za a tafi da wata takardar shaida musamman takardar haihuwa ta Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ko kuma takardar zama dan asalin karamar hukuma ko jiha zuwa ofishin yin rajistar.
  4. A nan kuma za a dauki bayanan mutum kamar tsawo, hoton zanen yatsu da dai sauransu.
  5. Daga nan ne kuma za su ba wa mutum takardar shaida ta wucin gadi kafin katin na ainihi ya fito.