✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zaben fid-da-gwanin PDP zai gudana

Ba za a yi zaben fid-da gwanin sanatoci a yankin Kudu maso Gabas yadda aka tsara da farko ba.

Jam’iyyar PDP ta sanar da cewa a ranar Asabar za ta gudanar da zaben fid-da-gwani na wadanda za su tsaya mata takara a zaben 2023.

Karo uku ke nan jam’iyyar na dage zaben tsayar da ’yan takarar, sai dai a wata takarda da jam’iyyar ta aike wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta bayyana sababbin ranakun da ta tsayar na zaben fitar da ’yan takarar majalisun jihohi da na tarayya da na gwamnoni.

Sababbun ranakun sun nuna za a gudanar da zaben ’yan takarar majalisun jihohi a ranar Asabar, sai kuma na ’yan Majalisar Wakilai zai gudana a jibi Lahadi.

Kazalika, sanarwar ta ce za a yi zaben fid da ’yan takarar sanatoci a ranar Litinin 23 ga Mayu, inda za a yi zaben fid-da ’yan takarar gwamnoni a ranar Laraba 25 ga Mayun da muke ciki.

A wasikar da Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa, Farfesa Iyochia Ayu da Sakataren Jam’iyyar Mista Samuel Anyanwu suka rattaba wa hannu, ta ce ba za a gudanar da zaben fid da ’yan takarar sanatoci a Kudu maso Gabas a ranar Litinin ba, saboda dokar zaman gida da ’yan awaren Biyafara suka sa a kowace Litinin a yankin.

Bayanai sun ce sauran jam’iyyun siyasa ciki har da Jam’iyyar APC mai mulki suna ta kamun kafa don ganin hukumar zabe ta kasa ta kara wa’adin gudanar da zaben fid-da’yan takarar.