Daily Trust Aminiya - Yadda zanga-zangar #EndSARS ta sa Direbobi da fasinjoji tafk
Subscribe

Masu zanga-zangar #EndSARS

Yadda zanga-zangar #EndSARS ta sa Direbobi da fasinjoji tafka asara

Direbobin motocin haya da fasinjoji sun tafka asara sakamakon rufe hanyoyi da masu zanga-zangar #EndSARS su ka yi.

Masu zanga-zangar sun datse babban titin Kubwa da hanyar filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, wasu ne daga cikin manyan hanyoyin da ke fita ko shiga Abuja daga wasu sassan Najeriya.

Alhaji Bara’u, daya daga cikin direbobin da zanga-zangar ta rutsa da su a hanyar Kubwa, ya koka da yadda hakan ya ja masa asara.

“Na sha fetur da kudin fasinja ga kuma tafiyar ta kai mu yamma, wasu fasinjojin sun ce sun fasa tafiyar, a ba su kudinsu,” inji shi.

Bara’u ya ce lodin fasinjojin Kaduna ya yi, amma mutane hudu sun fasa tafiyar sun karbi kudinsu.

“Yanzu mutum biyu kacal suka amince mu kama hanya idan an bude kafin karfe shida. Sauran mun raba asara sun karbi kudin motarsu.”

Daya daga cikin fasinjojin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tun karfe 2:00 na rana suka bar tashar motar Jabi da niyyar zuwa Kaduna da wuri.

“Allah kuma kadai ya san lokacin da za mu bar nan”, inji shi.

Juyen fasinja

Direbobin bas-bas kuwa sun rika juye ne a hanya saboda karancin fasinjoji.

Direbobin bas-bas da ke jigilar fasinjojin Zuba da Madalla da Suleja sun shiga tsaka mai wuya yayin da masu zanga-zangar suka datse hanyar ta Kubwa.

Wakilin Aminiya ya ga wasu kwandastocin mota suna tsallakawa domin samo fasinjojin da suka sauko ko kuma su nemi fasinjojin da za su juya da su cikin gari.

Kazalika, wasu daga cikin fasinjojin kan yafe kudin motar da suka biya su nemi wata a daya bangaren.

Yusuf Usama, daya daga cikin fasinjojin da ke takawa a kafa. ya koka kwarai da halin da masu zanga-zangar suka jefa shi a ciki.

‘Abu ya zama masifa’

“Wannan abu ya zama masifa. Hakan ya saba wa yadda ake gudanar da zanga-zanga.

“A can baya sun sace iskar tayar motar da na shiga saboda direban ya ce bai kamata su tare hanya ba,” inji Usama.

Ya ce ya baro wajen ne domin kaucewa rikicin da ka iya barkewa tsakanin direban da masu zanga-zangar.

“Idan ka lura duk mashaya ne, kuma komai na iya faruwa,” inji shi,

More Stories