✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Zulum ya rage wa masu ice hanya da motar gwamnati

Shi da kansa ya sauko ya sa motocin su dauke su da icensu zuwa gida

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya tsayar da ayarin motocinsa, inda ya rage wa wasu yara da ya gani sune neman icen girki a cikin daji hanya.

Zulum ya hango ’yan matan su 12 ne suna kokarin daukar icen da suka yi a yayin da motocinsa ke wucewa a garin Monguno, a ranar Litinin, kuma nan take ya sa a tsaya.

Wani daga cikin hadiman gwaman, Abdurahman Bundi, wanda ke cikin ayarin ya ce, “Dukkanmu mun yi mamakin abin da ya sa shi ya tsayar da mu yana sane da ayyukan Boko Haram a kan hanyar.

“Gwamnan ya fita daga motarsa ya tafi kai tsaye zuwa wurin da ’yan matan suke tsaye, ya tambaye su me suka zo yi a wurin mai nisan kilomita 15 daga garin Monguno.

“Sai ya umarci wasu daga cikin motocin da ke cikin ayarin su dauki yaran tare da icen da suka yi, su kai su Monguno,” inji shi.

Yawancin mutanen Monguno sun koma amfani da ice a matsayin makamashin girki da jin dumin iyalai, tun bayan da mayakan Boko Haram suka ragargaza garin.

Hanyar Maiduguri zuwa Monguna na yawan fama da mayakan Boko Haram inda suke kafa shinge a wasu wurare su kwace wa matafiya dukiyoyi.