✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yahaya Bello ya zama dan takarar da ya fara sayen fom din APC a kan N100m

Ana sa ran zai karbi fom din ranar Laraba

Daya daga cikin ’yan takarar Shugabancin Kasa a jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya zama mutum na farko da ya biya Naira miliyan 100 don sayen fom din takarar Shugaban Kasa.

Ana sa ran zai karbi fim din nasa ranar Laraba.

Gwamnan ya biya wadannan kudi ne a safiyar Talata, inda ya zamo dan takarar da a hukumance ya fara siyan fom a jam’iyyar, kamar yadda sanarwar da Daraktan Yada Labaran kungiyar yakin neman zabensa, Yemi Kolapo, ya fitar.

Yahaya Bello dai ya bayyana aniyarsa ta fitowa takara ne tun a ranar biyu ga watan Afrilu, duk da cewa ya fito ne daga jihar da ke arewa ta tsakiya, da kuma kiraye-kiraye da jam’iyar ta su ke sha na fito da dan takararta daga Kudancin kasar.

A sanarwar da Kolapo ya fitar, ya ce yanzu ne hankalin magoya bayan Gwamna Yahaya Bello zai kwanta domin sayen fom din ya sake tabbatar wa ’yan Najeriya da gaske yake.

Haka kuma, ya ce sun samu kwarin gwiwa ne la’akari da yawan Gwamnoni da jagorori, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar da suka nuna goyon bayansu ga dan takararsa.

Daraktan ya ce Yahaya Bello ba zai ba ’yan Najeriya kunya ba muddin suka ba shi dama, kasancewar ba shi da tarihin cin amana.

Daga nan sai ya yi kira ga daliget-daliget na jam’iyyar da su yi watsi da duk wasu batutuwan da za su iya kawo rarrabuwar kawuna domin ci gaban Najeriya.