✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin Aiki: ASUU ta bai wa gwamnatin Najeriya wa’adin mako uku

ASUU ta ce babu wani zabi da ya rage mata saboda ta gaji da gafara sa ba ta ga kaho ba.

Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU) ta bai wa gwamnatin kasar wa’adin mako uku ta cika alkawarin da ta yi na biyan wasu bukatun ’ya’yanta ko kuma su shiga yajin aiki.

Kungiyar ta yanke shawarar bai wa gwamnati wa’adin ne a wani taron Majalisar Kolinta da ta gudanar ranar Litinin a Abuja.

Kungiyar ASUU ta bayyana cewa ta yanke shawarar bai wa gwamnati mako uku ne ko ta cika alkawarin da ta yi wa ’ya’yanta yau tsawon shekara.

ASUU ta ce muddin ba haka ba za ta umurci ’ya’yanta da su shiga yajin aiki na sai abin da hali ya yi, saboda sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.

Shugaban kungiyar na Kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya jagoranci zaman ya ce ba su da zabi face ba da wa’adin.

Farfesa Osodeke ya ce wajibi ne gwamnatin ta cika masu alkawarran da su ka sanya wa hannu yayin zaman da suka da ita tun ranar 23 ga watan Disamban 2020.