✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya ta gayyaci ASUU taron gaggawa

ASUU ta yi barazanar komawa yajin aikin da ta dakatar saboda abin da ta kira cin zarafin mambobinta.

Ministan Ilimi na Najeriya, Adamu Adamu, ya gayyaci wakilan Kungiyar Malaman Jami’o’in kasar (ASUU) zuwa taron gaggawa, bayan barazanar sake shiga wani yajin aiki da kungiyar ta yi.

Za a gudanar da taron na gaggawa da misalin karfe 11.00 na safiyar Talata, 6 ga watan Afrilun, 2021.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarain Ma’aikatar Ilimi, Ben Bem Goong ya fitar, ta ce za a gudanar da taron ne a Hedikwatar Ma’aikatar da ke birnin Abuja.

Yayin bayyana dalilinsa, Ministan ya ce an kira taron na gaggawa ne domin dinke barakar da ke iya kaiwa ga malaman jami’ar su shiga yajin aikin da suke shirin yi.

ASUU ta yi barazanar sake komawa yajin aikin da ta dakatar ne saboda abun da ta kira cin zarafin da ake yi wa mambobinta da kuma kin biyan su albashinsu na tsawon wata 10.

Ana iya tuna cewa, a watan Janairun da ya gabata ne ASUU ta janye yajin aikinta na wata tara bayan daidaitawa da Gwamnatin kan wata muhimmiyar yarjejeniya da ta shafin bukatun malaman.