✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aiki: Kayan abinci sun yi tashin gwauron zabo a Kudu

Mahauta da ’yan kasuwar da ke da ragowar kayan na cin karensu ba babbaka ta hanyar tsawwala farashi.

Kayan abinci da nama na neman gagarar mutane a Kudacin Najeriya sakamakon yajin aikin da masu sayar da kayan ke yi a fadin Najeriya.

Yajin aikin da gwamayyar masu kayan abinci da dabbobi ta kasa (AUFCDN) bayan cikar wa’adin da ta ba Gwamnatin Tarayya na biyan bukatunta ya sa farashin kayan tashin gwauron zabo.

Matakin na hana tsallakawa da kayan daga Arewa zuwa Kudu ya sa mahauta da ’yan kasuwar da ke da ragowar kayan cin karensu ba babbaka ta hanyar tsawwala farashin.

Aminiya ta gano cewa yanzu farashin kwandon tumatir ya tashi daga N4,000 zuwa N15,000, kilon naman sa kuma daga N1,200 ya koma N2,000 a Legas, Jihar da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce a can ake cin fiye da rabin naman da ake samarwa a Najeriya.

Shugaban kungiyar mahautar Oko-Oba a yankin Agege a Jihar, Abdullahi Ahmed ya ce suna yanka shanu 1,000 a kullum a mahautar, ranar Asabar kuma akan yanka kusan 1,500.

Amma, “Yanzu karancin shanu ya sa ba ma iya yanka 200; Wadanda muke yankawan ma a nan ake kiwata su kuma kanana ne,” inji shi.

Ya shaida wa Aminiya cewa shanu ukun da ya yanka ranar Asabar ya saye su ne a kan N630, 000.

“Na ga sa daya da aka saya N900,000 ranar Asabar. Abin ya yi tsanani sosai,” inji shi.

Mun kuma samu bayani cewa cewa shanu biyar aka yanka a mahautar  Odo-Eran  a yankin Barikin Sojoji na Ojo a ranar Asabar.

Wata ’yar tireda a Kasuwar Agbara da ke kan iyaka a Jihar Ogun, Chineye Okoroafor ta ce yanzu ’yan kasuwa sun koma boye kaya.

Aminiya ta gano cewa yanzu yawancin mutane masu bukatar nama sun koma sayen kifi, masu so su sayi kayan miya su adana kuma abin ya gagara.

AUFCDN wanda ke karkashin Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta shiga yayin aikin ne tana bukatar diyyar Naira biliyan 475 na dukiyoyi da rayukan ’ya’yanta da aka salwantar a lokacin tarzomar EndSARS a Kudancin Najeriya da kuma rikicin kabilanci a Ibadan.

Tana kuma bukutar Gwamnatin Tarayya ta janye shingayen binciken ababen hawa a manyan hayoyi, saboda zargin cin zalin ’ya’yanta da kuma tatsar su kudade da jami’an tsaro ke yi a shingayen.

Tashin gwauron zabo a kasuwar Sasa

A Kasuwar Sasa da ke Ibadan, inda rikicin kabilnacin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa daga Arewa ya kuma taimaka wajen haifar da yajin aikin, farashin kaya sun yi mummunan tashi.

Kasuwar Sasa babbar matattara ce ta manyan motocin da ke jigilar kayan abinci irin su tumatir, albasa da barkono Arewacin Najeriya zuwa Jihar Oyo.

Wata mata a unguwar Agodi, Yinka Ojebode ta ce, “Farashin albasa ya fara komawa yadda yake, sai kuma ga rikicin na Sasa ya shafi sauran kayan miyan.”

Babajola na Kasuwar Sasa, Cif Popoola Rasheed ya musanta rahotannin da ke cewa wasu ’yan kasuwa Hausawa sun ki komawa kasuwar.

“Dukanmu mun halarci Sallar Juma’a a ranar Juma’a. Limamin Hausawa ya jagoranci rukunin farko, rukuni na biyu kuma limamin Yarbawa ya jagorance su,” inji shi.

Daga Sagir Kano Saleh; Abiodun Alade, Christiana T. Alabi, Eugene Agha, Abdullateef Aliyu (Legas); Jeremiah Oke, Ibadan, Victor Edozie (Fatakwal); Bola Ojuola, Akure; Peter Moses (Abeokuta); Usman A. Bello, Benin; Raphael Ogbonnaiye, Ado-Ekiti; Iniabasi Umo, Uyo; Eyo Charles, Kalaba; Bassey Willie, Yenagoa; Jude Ohajianya, Owerri; Titus Eleweke, Awka & Idowu Isamotu, Abuja.