✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin Aiki: Ma’aikacin Jami’a ya kashe kansa saboda kuncin rayuwa

Ma’aikacin ya shiga matsalar rashin kudi a bayan nan.

Wani ma’aikaci na Jami’ar Benin mai suna Carter Oshodin ya kashe kashe kansa a Jihar Edo saboda kuncin rayuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin ma’aikacin ya yi wannan aika-aika ne sakamakon matsalar rashin kudi da ya rika fuskanta a bayan nan.

Wannan dai ya faru ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da haramta wa ma’aikatan jami’o’i albashinsu saboda yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, gabanin faruwar lamarin, marigayi Carter wanda daya ne daga cikin wadanda yajin aikin ASUU ya shafa, ya rika koken kuncin rayuwa da har ta kai ga yana rokon makwabtansa taimakon kudi.

Wani daga cikin abokansa a shafin Facebook mai suna Edward, ya bayyana cewa marigayin ya shiga cikin matsananciyar damuwa musamman saboda yadda ya gaza biyan kudin makarantar ’ya’yansa mata biyu.

Tuni dai rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta bakin mai magana da yawunta, Chidi Nwabuzor ta tabbatar da faruwar lamarin duk da a cewarta ba a shigar mata da rahoton faruwarsa ba a hukumance.

“Eh, tabbas mun samu labarin faruwar lamarin amma ba iyalan mamacin ne suka sanar da mu ba.

“Har ya zuwa yanzu babu wanda ya shigar mana da rahoton faruwar lamarin a hukumance, amma dai mun samu labari ta hanyar bibiyar abubuwan da ke faruwa a jihar.”