✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yajin aiki: TUC ta roki ASUU ta sassauta matsayarta

TUC ta bukaci ASUU ta sassauta domin samun matsaya ta yin maslaha.

Kungiyar ‘Yan Kasuwa (TUC) kuma mamba a Kungiyar Kwadago ta Kasa, ta roki Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU a kan ta sassauta bukatanta don cimma matsayar da za ta ba da damar dalibai su koma makaranta.

TUC ta yi wannan roko ne ta bakin shugabanta na reshen Jihar Ribas, Mr Monday Ogbodum, yayin tattaunawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Talata a birnin Kalaba.

Ogbodum ya ce ASUU ta riga ta sanar da duniya bukatunta da yajin aikin da take kan yi, don haka ya shawarci gwamnati da ta daina bari sai an kai ga shiga yajin aiki kafin daukar matakin magance wata matsala.

Ya kara da cewa, duba da muhimmancin jami’o’i bai kamata yajin aiki ya zama hanyar warware matsala ko cimma bukatun ma’aikata ba.

Haka nan, ya ce abu ne mai wahalar gaske a cimma abubuwan da aka rasa a tsarin ilimin jami’o’i a shekaru biyun da suka gabata sakamakon yajin aikin malaman jami’o’i.

Kazalika, Ogbodum ya ce ba daidai ba ne amfani da tsarin ‘ba-aiki-ba-albashi’ da gwamnati ke yi don hukunta malaman jami’oin da suka ki komawa bakin aiki.

(NAN)