✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin ASUU: Dalibai sun nemi sarakuna da malamai su sa baki

Kungiyar Dalibai ’Yan Kabilar Tangale Waja a Jihar Gombe (TAWASA) ta roki malaman addini da sarakunan gargajiya da su shiga tsakani a kan yajin aikin…

Kungiyar Dalibai ’Yan Kabilar Tangale Waja a Jihar Gombe (TAWASA) ta roki malaman addini da sarakunan gargajiya da su shiga tsakani a kan yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke ci gaba da yi.

Daliban sun yi wannan kira ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Shugaban Kungiyar na kasa, Kwamred Dalibi S Biti, da suka raba wa da manema labarai a Gombe.

Kungiyar ta ce matsalar yajin aiki da aka jima ana yi ta ishi daliban kasar nan ba ma na Gombe kadai ba, inda suke kira da a janye shi don su samu su koma makarantunsu.

Har ila yau, kungiyar ta sake yin kira ga ASUU da Gwamnatin Tarayya da kuma duk masu ruwa da tsaki da su sa baki dan kawo karshen yajin aikin.

Kwamred Dalibi S Biti, ya kuma hori daliban a lokacin da suke zama a gidan da cewa kar su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen zama ’yan bangar siyasa daga baya su zo suna cizon yatsa.

Dangane da babban zabe dake tafe kuwa, ya hori daliban musamman Yan asalin Gombe ta kudu daga Tangale Waja da su zabi shugabanni masu kishin raya ilimi da kuma ganin sun ciyar da matasa gaba.

Daga nan sai Shugaban kungiyar ya gode wa kokarin daidaikun al’umma na yadda suke tallafa wa daliban ta hanyoyi daban-daban.