✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar KASU ta umarci dalibai su koma aji

Jami'ar ta bai wa dalibai da malamai kwanan watan komawa daukar darasi.

Hukumar gudanarwar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta umarci dalibanta da malamai su dawo daga ranar 9 ga Mayu, 2022 don ci gaba da darussa.

Jami’ar ta sanar da ficewarta daga yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ke ci gaba da yi kan zargin Gwamnatin Tarayya da gaza cika wasu alkawura da ta yi mata.

Jami’ar ta fitar da wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Afrilu da kuma sa hannun Sakataren Ilimi na Jami’ar, Abdullahi Zubairu.

Hukumar gudanarwar makarantar ta umarci dukkan dalibai da malaman makarantar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu.

Ta shawarce su da su bi jadawalin tsarin karatu da suke ciki.

A baya, Aminiya ta bayyana yadda Ministan Kwadago da Inguntuwar Aiki, Chris Ngige, a baya-bayan nan ya ce ASUU ce kadai za ta iya kawo karshen yajin aikin da ta ke yi.

“Komai yana hannun ASUU; su ne za kadai za su iya kawo karshen yajin aikin.

“Yana da kyau su duba irin abubuwan da kwamitin Benimi Briggis ke yi don kara wasu bayanai wajen kawo karshen wannan takaddamar,” in ji ministan.