✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin ASUU: Kungiyoyi 47 sun shiga zanga-zangar NLC a Kaduna

ASUU ta sha alwashin ba za ta janye yajin aiki ba har gwamnati ta biya mata bukatunta.

Kimanin kungiyoyin ‘yan kasuwa 47 ne suka shiga zanga-zangar da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta gudanar ranar Talata a Jihar Kaduna.

NLC dai ta shirya zanga-zangar ce domin goyon bayan Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ke gudanar da yajin aikin neman Gwamnatin Tarayya ta biya mata bukatunta.

Zanga-zangar, wadda ta gudana karkashin jagorancin shugaban NLC na Jihar Kaduna, Kwamared Ayuba Suleiman, an yi tattaki zuwa Majalisar Dokokin jihar inda aka rika waken tabbatar da hadin kai wajen nuna rashin jin dadinsu kan rashin biyan bukatun ASUU.

Da yake jawabi ga Mataimakin Kakakin Majalisar, Honarabul Isaac Auta Zankai,  Kwamared Ayuba ya ce, zanga-zanga ita ce kadai yaren da gwamnatin Najeriya ke fahimta.

Ya kara da cewa, za su bai wa ASUU cikakken goyon bayansu har sai Gwamnatin Tarayya ta yi abin da ya kamata.

A cewarsa, “Wannan al’amari ne mai matukar muhimmanci, muna bukatar ‘ya’yanmu su koma makaranta domin kuwa ba mu da karfin da za mu tura su karatu kasashen ketare.”

Haka nan, Ayuba ya jaddada yadda kungiyarsu ta damu da halin da gwamnatin ke nunawa na kin magance matsalolin da suka haifar da yajin aikin ASUU.

Da yake karbar masu zanga-zangar, Honorabul Zankai ya yi godiya ga shugabannin kungiyar bisa hakurin da suka nuna, yana mai cewa “babu wanda ke jin dadin yadda dalibai ke zaman gida, burinmu shi ne mu ga yara sun koma makaranta,” inji shi.

Idan dai ba a manta ba, Shugaban NLC na Kasa, Kwamred Ayuba Wabba, ya bai wa NLC na jihohin kasar nan umarni a kan su fito zanga-zangar nuna goyon baya ga ASUU a Talatar nan har sai Gwamnatin Tarayya ta yi abin da ya kamace ta, yayin da shi da kansa zai jagoranci zanga-zangar a Abuja da za a gudanar a ranar Laraba.

Sama da wata biyar kenan da ASUU ta soma yajin aiki inda take neman Gwamnatin Tarayyata ta biya mata tarin bukatun da ta sha alwashin ba za ta janye yajin aikin ba har sai an biya mata su.