✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yajin aikin ASUU masalaha ce ga ’ya’yan talakawa —Sheikh Sani Fagge

Idan ASUU ta janye, ‘ya‘yan masu kudi ne kadai za su iya karatun jami'a.

Yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’oin Najeriya (ASUU) ke ci ci gaba da gudanarwa masalaha ce ga ’ya’yan talakawa a cewar Shehun Malamin addinin Islama, Umar Sani Fagge.

Shehun malamin wanda kuma Farfasa ne a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ya fadi haka ne a cikin wani jawabi da ya yi kwanan nan da a yanzu ake yadawa a Intanet.

Malamin ya ce, idan kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da ta ke yi ba tare da a cimma matsaya ba, ‘ya‘yan masu kudi ne kadai za su iya karatun jami’a, domin a cikin kashi dari, kashi goma ne za su iya ci gaba da karatun.

A cewarsa, yajin aikin da aka shafe wata da watanni ana yi, ba don masalahar malaman jami’a ba ce, da masalaharsu ce da tuni sun hakura sun janye.

“Duk wanda aka shafe fiye da watanni biyar ba a biyansa albashi kuma ya hakura, kai ka san akwai manufa mai kyau a ciki,” in ji shehun Malamin.

Farfesan ya kuma bayyana takaici kan yadda gwamnati ke neman yin watsi da karatun daliban jami’a “kuma a hakan ma, malaman jami’a su suka san irin bala’in da dalibai suke ciki  yanzu.

“A yanzu da kyar wasu daliban jami’ar ke iya biyan kudin rajistar karatu na naira dubu talatin ko dubu arba’in, wanda idan ba a yi farga ba, zai iya komawa miliyoyin naira.

“A yanzu karatun jami’a yana cikin rudani la’akari da cewa gwamnati ta mayar da wasu abubuwan inganta rayuwa hannun ’yan kasuwa irinsu samar da wutar lantarki da man fetur da sauransu.

Malamin ya yi kira ga jama’a da su tashi da addu’a kan Allah Ya ganar da gwamnati kan ta yi abin da ya dace wanda zai taimaka wa talaka.