✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yajin aikin ASUU: Rashin kwarewar Ministan Ilimi ne —Atiku

Shekarau ya kawo karshen yajin aikin ASUU cikin mako uku, a matsayin ministan Ilimi

Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya dora laifin yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ke gudanarwa a Najeriya kan rashin kwarewar Ministan Ilimi, Adamu Adamu.

A hirar da gidajen rediyo suka yi da shi ranar Talata da dare a Kano, Atiku ya zargi Gwamnatin Tarayya da rashin daukar yajin aikin jami’o’in da muhimmanci, shi ya sa ba ta mayar da hankali ta kawo karshensa ba.

Atiku ya ce, “Akwai babban rashin fahimtar yadda ake gudanar da jami’o’i a Najeriya; Yanzu jami’o’in Gwamnatin Tarayya na yakin aiki.

“Ina tattauna da Malam Ibrahim Shekarau, wanda tsohon Ministan Ilimi ne, ya bayyana mini cewa a lokacin da aka nada shi minista ASUU na yakin aiki, amma ba a yi sati uku ba ya daidaita da su suka dawo bakin aiki.

“Akwai rashin kwarewa a tattare da ministan Ilimi [na yanzu] saboda shi ke da alhakin shiga tsakani ya daidaita lamarin.

“Ba zan ce lallai ga wanda ya di laifi ba [a cikin bangarorin biyu] amma na yi amanna cewa Gwamnatin Tarayya ba ta dauki abin da muhimmanci ba.

Zargin nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan ASUU ta mayar da yajin aikin da ta shafe wata shida a ciki zuwa na sai baba ta gani.

ASUU ta shiga yajin aikin sai baba ta gani ne bisa zargin Gwamnatin Tarayya ta kin cika ko daya daga cikin alkawura da ta yi wa malaman jami’a bayan bangarorin biyu sun cim-ma yarjejeniya.

Atiku wanda ya ke Kano tun ranar Lahadi ya zargi gwamnatin Jamhuriyar APC mai mulki na shekara bakwai da kara jefa Najeriya cikin matsalar rashin tsaro da da karin talauci.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ziyarci Jihar Kano ne domin karbar tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa da suka sauya sheka daga Jam’iyyar NNPP zuwa PDP,

“Babu wani abin kirki da gwamnatin APC ta tabuka; abubuwan da take yi sun saba alkawuran da ta yi wa ’yan Najeriya.

“Ina ganin lokaci ya yi na ’yan Najeriya su tashi su kawar da mulkin APC su dawo da PDP, saboda abubuwan da PDP ta yi sun fi karfin a kwatanta da na APC,” in ji shi.