✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yajin aikin ASUU ya karya harkokin kasuwancinmu’

Nakan yi wa mutane sama da 20 yankan farce. Amma a yanzu da kyar nake yi wa mutum biyu zuwa uku.

A daidai lokacin da aka kwashe kimanin wata bakwai da shiga yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), mutane sun fi mayar da hankali kan illar hakan ga dalibai da ake ganin suna samun koma-bayan karatunsu da kuma malamai da aka daina biya albashi.

A kwanakin baya Aminiya ta ruwaito yadda malaman jami’o’in suke rayuwa cikin kunci, inda wasu suka bayyana cewa an daina ba su bashi, wasu kuma suna sayar da kadarorinsu wasu ma sun kama wasu sana’o’i ko kasuwanci.

Sai dai Aminiya ta lura ba a cika magana a kan masu harkokin kasuwanci a ciki da wajen harabobin jami’o’in ba, wadanda da yawansu nan ne kadai hanyar samun abincinsu.

Hakan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin halin da irin wadannan mutane suke ciki bayan kwashe watanni ba tare da harkokinsu suna tafiya ba.

Yadda lamarin yake a Jami’ar Bayero

A Jami’ar Bayero da ke Kano, tuni wasu daga cikin masu sayar da kayayyaki a harabar jami’ar suka rufe shagunansu saboda rashin ciniki inda kuma wadanda suka rage suna kasuwanci suke gudanarwa a cikin wani yanayi mara dadi.

Muhammad Hussain da ke sayar da kayan masarufi a cikin jami’ar ya ce yajin aikin ya janyo wa harkokin kasuwancinsa koma-baya wanda hakan ya shafi rayuwarsa da ta iyalinsa.

“Harkokin kasuwanci sun tsaya cak. A da muna yawan zuwa kasuwa amma a yanzu sai mu yi wata ba mu je kasuwa ba.

A yanzu lamarin sai addu’a. Ki duba ki ga shagona duk kayan ciki sun kare kuma babu kudin da za a zuba wasu domin da kudin ake cin abinci da sauran bukatu na yau da kullum.

“A yanzu haka muna bude shagon ne don kada mu zauna a gida. Ga shi jarin nawa ya karye domin a baya shagona cike yake da kaya sabanin yanzu da komai ya kare,” inji shi.

Ya yi fatar za a samu daidaito a tsakanin malaman jami’o’in da gwamnati cikin gaggawa don dalibai su dawo makaranta, “Mu ma masu kasuwanci harkokinmu su farfado,” inji shi.

Idris Sani da ke gudanar da aikin gurza takardu ya ce yajin aikin ya rusa masa shirin da yake yi game da kasuwancinsa.

Ya ce a baya lokacin da ake karatu sukan yi cinikin Naira dubu 10 a kulllum amma ayanzu da kyar suke samun kudin mota.

“Hatta abinci wani lokacin ba mu samu mu saya saboda rashin cinki,” inji shi.

Ya yi kira ga malaman jami’o’in su rage buri don a samu daidaito a tsakaninsu da gwamnati a kawo karshen wannan dogon yajin aiki, “Da ya jefa rayuwarmu cikin wani hali,” inji shi.

Wani mai sayar da turare a Jami’ar Bayero, mai suna Imran Ahmad ya ce yajin aikin ya janyo masa ci baya a harkokin kasuwancinsa.

Ya yi kira ga Kungiyar ASUU da gwamnati su daidaita domin harkokinsu su dawo.

Ya ce “Muna kira ga gwamnati ta duba bukatun malaman domin a samu a kawo karshen wannan yajin aiki.”

Sulaiman Abdullahi mai sayar da kayan marmari a harabar Jami’ar Bayero ya ce, “Duk da yake a yanzu muna dan taba ciniki, to amma kasuwancinmu ya koma baya sosai.

A baya da ake karatu mukan yi ciniki sosai sabanin yanzu da da kyar muke sayar da kayan Naira 500 ko 600 ko dubu daya.”

Wani mai yankan farce mai suna Usaini Adamu ya ce yajin aikin ya sanya rayuwarsa ta shiga kunci sakamakon rashin samun aiki da yake fama da shi.

“A da nakan yi wa mutane sama da 20 yankan farce. Amma a yanzu da kyar nake yi wa mutum biyu zuwa uku,” inji shi.

Malam Abbas Abdulhameed mai harkar hada-hadar kudi ne a POS a Jami’ar Bayero, ya bayyana yadda yajin aikin ya janyo masa koma baya a harkarsu.

Ya ce, “Mutane suna dan shigowa cikin makaranta kuma sukan nemi kudi amma abin bai kai baya ba domin lokacin da dalibai suke nan a kullum nakan yi hada-hadar kudi ta kusan Naira miliyan daya amma yanzu da kyar ake yin dubu dari.”

Yadda lamarin yake a Jami’ar Ahmadu Bello

A Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, yajin aikin malaman jami’o’in ya haifar da matsaloli a fannin tattalin arzikin masu saye da sayarwa a cikin jami’ar da kuma makwabtanta.

Wakilinmu ya zagaya cikin jami’ar, inda ya gano cewa matsalar ta fi shafar masu hada-hadar kasuwanci da masu harkar sufuri a jami’ar.

Shu’ibu Dan Arewa wanda yake da shagon sayar da kayayyaki a Jami’ar ABU din ya ce kafin a fara yajin aikin a duk rana yakan yi cinikin da bai gaza Naira dubu 10 ba, amma yanzu da yakan dan leka shagon ko Naira dubu daya da kyar yake iya yi a kullum.

Shi kuwa wani da ke sana’ar gurza takardu ya ce sun kasance cikin kunci ne saboda sun dogara da dalibai da kuma ma’aikatan jami’ar don samun abin masarufi su da iyalansu.

Wani mai shagon makulashe mai suna Alhaji Garba Sadauki ya ce wannan yajin aikin su ake yi wa saboda a da yana harkoki sosai, amma saboda yajin aikin kasuwarsu ta zama tamkar garin da ruwa ya ci domin wasu da dama sun rufe wuraren harkarsu.

A bangaren sufuri kuwa, abin ya yi kamari domin masu Keke-NAPEP da babura da motocin haya da ke cabawa a baya, yanzu ko layin masu lodi da ake gani babu.

Wani dan Kungiyar Sufuri ya bayyana wa Aminiya cewa babu wanda yajin aikin bai shafa ba. Wakilinmu ya zagaya cikin harabar jami’ar da ke Samaru da Kongo, inda ya gane wa idonsa yadda harabobin suka yi tsit.

Haka ma ta fuskar wadanda suke bayar da hayar gidajen kwana ga dalibai yajin aikin ya shafe su.

Haruna Musa Janwai daya ne cikin masu samar wa dalibai hayar dakuna, ya ce yajin aikin ya kai su ga fitar da wasu kadarori suna sayarwa domin su samu abin sa wa a baki.