✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin ASUU zai zama tarihi idan na zama Shugaban Kasa —Atiku

Mahaifina bai so naje makaranta ba, amma na jajirce na shiga makaranta har zuwa matakin jami’a.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce muddin ya zama shugaban kasa, kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ba za ta sake shiga yajin aiki ba.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a Juma’ar nan yayin magana a bikin Ranar Matasa ta Duniya a Abuja.

Ya ce mahaifinsa bai so yaje makaranta ba, amma daga baya ya jajirce da kuma shiga makaranta har zuwa matakin jami’a.

Wazirin na Adamawa ya kara da cewa, hakkin kowane matashi shi ne samun ilimi, inda ya ce yajin aiki da kungiyar ASUU ke yi da kuma rashin magance matsalar su da gwamnati ta gaza yi abin damuwa ne.

Ya kara da cewa, hakan ba za ta taba faruwa ba a karkashin gwamnatin PDP ko kuma gwamnatinsa idan aka zabe shi.

Kazalika, Atiku ya ce shi mutum ne mai bunkasa harkokin ilimi, yana mai cewa hakkin kowace gwamnati ne ta tabbatar an bai wa kowani matashi a kasar hakkokinsa musamman a bangaren ilimi.