✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yajin aikin Kaduna: NUPENG za ta shiga yajin gama-gari

Ma'aikatan man fetur na shirin shiga yayin aikin gama-gari kan takaddamar Kaduna

Kungiyar Ma’aikatan Fetur da Iskar Gas ta Kasa (NUPENGna shirin shiga yajin aiki a fadin Najeriya kan zargin jami’an tsaro da musguna wa ’yan kwadago da ke zanga-zangar lumana a Jihar Kaduna.

NUPENG ta kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta jan kunnen Gwamna El-Rufai gabanin abin da ta kira ‘taurin kansa da mayen giyar mulki’ su sanya lamarin ya kazanta kamar yadda ya saba yi ga duk lamarin da ya shafi jin dadin al’umma.

“Muna ankarar da dukkanin mambobin NUPENG da su zama cikin shirin ko-ta-kwana cewa a kowane lokaci za mu iya kiran su da su fara yajin aiki a duk fadin kasar nan, idan bukatar hakan ta taso,” inji sanarwar da Shugabanta na Kasa, Kwamred Williams Akporeha da Babban Sakatarenta Kwamred Afolabi Olawale, suka fitar.

NUPENG ta bayyana damuwa kan yadda macin lumanan da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) take yi yake rikidewa zuwa tarzoma saboda abin da ta kira mulkin kama karya na Gwamna Nasir El-Rufai.

NUPENG ta jaddada cewa kada a kuskura a nuna wa wani cikin shugabannin kungiyoyin kwadagon hantara ko kyara ko wani nau’in cin zarafi a yayin macin kwana biyar da NLC ke yi a Kuduna.

Kungiyar NLC ta shiga yajin aikin gargadi na kwana biyar kan korar dubban ma’aikata gwamnatin jihar da gwamnan ya yi.