✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yajin aikin likitoci: Sarkin Musulmi ya damu matuka

Sarkin Musulmi ya bukaci gwamnati da likitocin da su dawo teburin sulhu.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana matukar damuwa a kan yajin aikin likitoci a fadin Najeriya.

Sarkin Musulmin ya roki Kungiyar Likitocin Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin likitoci da ke karkashinta domin ba da damar tattaunawa mai muhimmancin tsakaninsu da gwamnati.

– Fashewar Gurneti ta hallaka yara 5 a Borno
– Buhari ya dawo daga Landan bayan kwana 18

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwar da Sarkin Musulmin ya sanya wa hannu ta hannu Daraktan Majalisar Koli ta Harkokin ta Addinin Musulunci, Zubairu Haruna Usman-Ugwu, a ranar Juma’a.

Sanarwar Sarkin Musulmin ta roki likitocin da su tuna rantsuwar aikin da suka yi da kuma irin yadda a halin yanzu cutran COVID-19 da kuma kwalara suke ta yi sanadiyyar asarar dimbin rayuka a fadin Najeriya.

Sarkin Musulmi ya kuma roki Ministan Kwadago, Chris Ngige, da ya sake tunani a kan matsayin gwamnati na dakatar da tattaunawar da suke da likitocin, duba da irin damuwar da dambarwar ta jefa ’yan Najeriya a ciki.

Sanarwar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta shiga tattaunawa ta gaskiya da shugabannin kungiyar likitocin, ta hanyar da za ta karfafa guiwa tsakanin bangarorin biyu, inda take cewa gwamnati na da alhakin shawo kan likitocin da kuma duba bukatunsu da kuma biyan bukatun ta hanyar da ta dace.

Sarkin Musulmin ya yaba da yunkurin majalisar dokoki kan yajin aikin tare da wasu ’yan Najeriya da suka nuna damuwarsu a kan lamarin, inda ya bukaci Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Ma’aikatar kwadago ta Tarayya da kuma likitocin da su koma kan teburin sulhu.