✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin likitoci ‘shirme’ ne —Ngige

Ministan Kwadago ya ba likitoci wa'adin janye yajin aiki ko a dakatar da albashinsu. Na gargadi 'ya'yana likitoci su kaurace wa yajin aiki —Ngige

Ministan Ayyuka da Kwadago, Dokta Chris Ngige, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta dauki tattsauran mataiki a kan likitocin da suka shiga yajin aiki.

Ngige ya ce yajin aikin da Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta shiga ‘shirme’ ne, don haka ya sa ’ya’yansa da ke aikin likita su kaurace masa.

Tun ranar Litinin likitocin suka fara yajin aiki bisa zargin Gwamnatin Tarayya da kin mutunta yarjejeniyar da ta kulla da su.

Bayan kokarin gwamnatin — ta hannun ma’aikatarsa — na ganin likitocin sun janye yajin aikin ya ci tura, Ministan ya sha alwashin daukar tsattsauran mataki a kansu idan ba su koma bakin aikinsu ba.

“Ina da ’ya’ya likitoci kuma na gargade su kan shiga wannan shirmen da sunan yajin aiki,” kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na Channels ranar Juma’a da dare.

Ya ba wa likitocin nan da mako mai zuwa su koma bakin aikinsu, idan ba haka ba gwamnati za ta dauki matakin “babu aiki, babu biyan albashi”.

“Ba zan sake yin zama da su ba saboda ina da wasu abubuwan a gabana. Na yi zaman sulhu sau biyu jiya. Shin zan ci gaba da bata lokacina ne ina zama da su?

“Ina da wasu ayyukan kuma a Ma’aikatar Kwadago kuma na sanar da NARD cewa ba za a biya su albashi ba a tsawon lokacin da suke yajin aikin.

“Saboda muhimmancinsu ga al’umma, bai kamata su fara yajin aiki ba ba tare da sun sanar da ni kwana 15 kafin ranar ba.

“Amma ban samu wata sanarwa ba daga gare su, shi ya sa na yi duba da sashe na 43 na Dokar Kwadago da kuma hakkin ma’aikaci.

“Abubuwa za su faru a mako mai zuwa. Su jira za su ga matakin da za a dauka. Suna wasa da rayukan al’umma babu dalili.

Ngige wanda shi ma likita ne, ya ce gwamnati ta dauki matakin da ya dace duk da rashin likitoci a bakin ayyukansu duba da yadda cutar COVID-19 ke kara tsananta a tsakanin al’umma.