✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yaki: Amurka za ta ba wa Ukraine tallafin Dala biliyan 33

Amurka ta ce tana tallafa wa Ukraine ne kadai don ta kare kanta daga hare-haren Rasha.

Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden, ya gabatar da shirin tallafin da ya kunshi Dala biliyan 33, don taimaka wa Ukraine da makamai domin yakar Rasha.

Biden ya gargadi Rasha cewa mika mata wuya ba zabi ba ne ga kasashen Yammacin Turai da Amurka.

Yayin da yake jawabi a fadar White House, Shugaba Biden, ya gabatar da kudurin wasu sabbin dokoki da za su bayar da damar amfani da kadarorin attajiran Rasha da aka kwace a karkashin takunkumin da aka kakaba musu.

Ya ce za a yi amfani da kadarorin wajen biyan diyya ga ’yan Ukraine, sakamakon barnar da sojojin Rasha suka yi musu, tun bayan yakin da suka kaddamar a watan Fabarairu.

Har wa yau, Biden ya kuma bayyana cewa tabbas Amurka na kashe makudan kudade wajen mara wa Ukraine baya a yakin da take yi da Rasha.

Sai dai, ya ce babu wani zabi da ya wuce ci gaba da gwagwarmayar dakile manufar Shugaban Rasha, Vladimir Putin, domin rashin yin hakan zai janyo asarar makudan kudaden da suka zarce na yanzu.

Dangane da zargin da jami’an Rasha da kafofin yada labaran kasar suka yi cewa sojojinsu na gwabza yaki ne da kasashen Yammacin Turai baki daya, a maimakon kasar Ukraine ita kadai.

Biden cewa ya yi har yanzu ba su taba kai hari kan Rasha ba, Amurka na taimaka wa Ukraine ta kare kanta ne daga mamayar Rasha da yi mata.

A kan matakin da katafaren kamfanin iskar gas na Rasha Gazprom ya dauka na katse iskar gas ga kasashen kungiyar tsaro ta NATO da kasashen Bulgaria da Poland kuwa, Biden ya ce Amurka ba za ta bar Rasha ta kuntata wa kasashen ba bisa ka’ida ba.