✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki da Boko Haram: ‘Ya kamata a hukunta kungiyar Amnesty’

Kungiyar Wayar da Kai kan Sha’anin Tsaro (CISA) ta bukaci a yi wa kungiyar kare hakki ta Amnesty International (AI) tsattsauran hukunci saboda zargin sojojin…

Kungiyar Wayar da Kai kan Sha’anin Tsaro (CISA) ta bukaci a yi wa kungiyar kare hakki ta Amnesty International (AI) tsattsauran hukunci saboda zargin sojojin Najeriya da ta yi da kashe tsoffin mutane a yaki da ta take yi da Boko Haram.

Shugaban CISA na Kasa, Chidi Omeje ya yi zargin cewa akasarin kungiyoyin kasashen waje da ke aiki a Arewa maso Gabas sun fi cutar da al’ummar yankin fiye da amfanar su.

“Akwai alamar tambaya a yadda kungiyar ta ba ta taba fitowa ta la’anci ayyukan ta’addancin da ake yi a Najeriya ba, ita ce ke zumudin ‘zuzzurfa bincike’ a kan mutanen da ta’addancin ya yi wa illa”, inji shi.

Ya bayyana haka ne a taron ’yan jarida a Abuja, a lokacin da yake martani ga rahoton da Amnesty International ta fitar wanda ke zargin sojoji da kashe tsofaffi a yankin Arewa maso Gabas.

Chidi Omeje ya ce rahoton abin takaici ne, ya kuma kara nuna manufar AI na zubar da kimar sojojin Najeriya duk da kokarinsu a yaki da Boko Haram.

“Rahoton na AI ya mayar da hankali wurin yi wa sojoji kazafin kai hari a kan tsoffin mutane a Arewa maso Gabas mai fama da ta’addanci.

“Muna zargin akwai mummunar manufa da aka boye a ciki, idan aka yi la’akari da irin gagarumar nasarar da aka samu ta yadda sojojin ke kiyaye ka’idar aiki a fadin kasar nana”, inji shi.

Ya ce yadda Amnesty International ta dukufa wurin aibata sojoin Najeriya ya kara tabbatar da manufarta na nema zububar da mutuncin Najeriya domin biyan wasu bukatunta.

Don haka ya bukaci Gwamnatin Taryya ta da binciki ayyukan Amnesty Interantional a Najeriya domin gano boyayyiyar manufar kungiyar ta kuma hukunta ta yadda ya kamata.

CISA ta kuma yi kira da a hanzarta yin dokoki da kuma tsara ayyukan kungiyoyin kasashen waje a cikin Najeriya ta yadda za a rika sanin hakikanin abubuwan da ke faruwa.