✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya: Nazari a mahangar Musulunci (3)

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a…

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a wani taro da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ a Babban Masallacin Egba, Kobiti, Abeokuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara.

 

Cin hanci da rashawa a Rundunar ’Yan sanda:

To fa, babbar magana, ka ji shakundum! Idan aka ce cin hanci da rashawa a rundunar ’yan sanda, to ta ina za mu fara? Ta karbar ‘na-goro’ ko ta cin zali, ko ta yin lalata da matan da aka tsare a caji-ofis ko kuwa ta mayar da fari baki wajen aiwatar da binciken wadanda ake zargi da laifi? Akwai wata shahararriyar magana da ake cewa, dan sanda abokin kowa, to amma haka abin yake a Najeriya? Mu dai a kasar nan, ’yan sanda tamkar abokan gabarmu suke saboda a mafi yawan lokuta za ka same su kiri-kiri suna mayar da fari baki da zarar an sinna musu ‘na-goro.’  Saboda mummunar ta’adar ’yan sandan Najeriya, ta kai har nagari daga cikinsu ba a la’akari da su a yayin bambance nagari da mugu, kudin goro kawai ake yi musu!

’Yan sanda masu kafa shingaye a titunanmu, suna amfani da wannan dama wajen amsar ‘na-goro’ daga masu ababen hawa ne kawai amma ba don kawo tsaro da jin dadin masu amfani da hanyoyin ba. Ba da na-goro ga ’yan sanda sai ya zama farilla, koda kuwa direba yana da cikakkun takardun motarsa; in kuwa ba haka ba su bata masa lokaci, in kuwa dan kiya-kiya ne kai, ka kasa hada na balas a wannan rana. Sun zama a wajen direbobi tamkar bawa da ubangidansa, sai yadda suka yi da su.

Abubuwan da suke janyo cin hanci da rashawa:

Wai shin me ke haddasa cin hanci da rashawa ne? Abubuwa da dama ne kan haddasa da kuma ta’azzara wannan mummunar dabi’a ta cin hanci da rashawa. Kadan daga cikinsu su ne rashin wadatar zuci ko rashin godiyar Allah da rashin samar da kyakkyawan tsari ga ci gaban matasa da talauci da kuma rashin aikin yi.

Rashin wadatar zuci ko rashin godiyar Allah na haifar da matsaloli da dama a mafi yawan kasashen duniya, ciki har da Najeriya. Wannan ya sa shugabanninmu na soja a lokacin mulkinsu da na siyasa ke daka wasoso a kan dukiyar ’yan kasa, wadda ya kamata a yi amfani da ita wajen gina al’umma amma su wawashe (ko kuma suna kan wawashewa) don gina kansu kawai; wanda hakan ya haifar da mummunar koma-baya ga kasar da kuma al’ummarta baki daya.

Rashin kyakkyawan tsari a ci gaban matasa da samar da wani takamaiman tsari ga matasa don su tsaya da kafafunsu, ya taka rawar gani wajen yawaitar rashin gaskiya da cin amana, kamar su yin damfara ta hanyar Intanet da fyade da sauransu a tsakanin matasan. Duk wadannan suna faruwa ne saboda gwamnatocin Najeriya sun kasa fahimtar muhimmancin taimaka wa matasa don neman na kansu. A duk lokacin da iyaye da gwamnatoci suka karfafi matasansu ta fuskar ba su tarbiyya da karfafa su ta hanyar koya ko inganta sana’ao’insu, to babu shakka za a dakile kaifin ko ma a kakkabe wannan annoba daga al’ummarmu baki dayanta.

Talauci, suka ce wai aminin kafirci! Ma’ana, duk inda ka ga talauci idan ka bincika da kyau, to za ka ga kafirci ko kuma burbushinsa. Karbabben kiyasi na duniya ya nuna cewa duk mutumin da yake rayuwa kasa da Dalar Amurka 1:25 (kimanin Naira 360.25), a rana, to za a iya cewa wannan mutumin talauci ya cim masa! To a Najeriya akwai mutane da dama da suke rayuwa a kan haka (N360.25), ko ma kasa da haka, wadanda hakan ya jefa su cikin aikata munanan dabi’u, ciki har da cin hanci da rashawa. Misali, inda za ka ga an tura mutum don ya kashe wani, don yin tsafi ko wani dalili na siyasa, a kan Naira dubu 10 ko kasa da haka, ko kuma ka ga ana amfani da matasa wajen bangar siyasa a kan kudin da ba su taka kara sun karya ba, duk saboda katutun da talauci ya yi wa matasa.

Rashin aikin yi daya ne daga cikin manyan kalubalen da suka dade da nanike wa ’yan Najeriya tsawon lokaci.  Mutane da dama sun auka cikin halin cin hanci da rashawa saboda rashin aikin yi da ya dade yana addabarsu. Abu ne mai sauki ga mutumin da yake zauna-gari-banza ya tsinci kansa cikin kowane irin rashin gaskiya da rashin imani don ya samu kudin da zai tallafi rayuwarsa da su, ta yadda daga karshe yin hakan ba zai haifar wa al’umma da mai ido ba.

Illolin cin hanci da rashawa wajen gina kasa:

Illolin suna da yawa amma kadan daga cikinsu akwai rashin zuba jari daga ’yan kasashen waje da yawaitar talauci da rashin ci gaban kasa da kuma yawaitar rikice-rikice a kasa.

Rashin aikin yi a Najeriya zai ragu matuka in da a ce an karfafa gwiwar masu zuba jari daga kasashen waje don su zo su zuba jarinsu. To amma sai ga shi masana’antun da suka kamata su zuba jarinsu a Najeriya suna ki yin haka saboda tsoron da suke da shi na rushewar dukiyarsu, ba ma maganar su samu riba ba saboda dalilin cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu, wanda hakan ya ta’allaka ga rashin tsaro da halin rashin tabbas da kasar ke fuskanta a koyaushe. Wannan ya sa ba sai mun fada ba, babu wani mai sanya hannun jari mai cikakken hankali da zai aminta ya zuba dukiyarsa a kasar da ta yi auren zobe da rashi tsaro!