✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Cadi na fuskantar matsala’

“Dole sai an hada karfi da karfe kafin a kawar da dukkan ’yan ta’adda daga yankin.”

Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa-da-kasa mai yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Cadi (MNJTF) ya ce wasu matsaloli sun bayyana a fagen daga a yunkurin da ake yi na kakkabe ’yan ta’adda.

Manjo Janar Abdul-Khalifah Ibrahim, wanda ya fadi haka ranar Lahadi yayin wata ziyara da ya kai wa Babban Hafsan Rundunonin Tsaro na Cadi, Laftanar Janar Abakar Daoud, ya ce gudunmawar kasar ta Cadi na da matukar muhimmanci wajen shawo kan wannan matsalar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato wata sanarwa da kakakin rundunar ta MNJTF, Kanar Mohammed Dole, ya fitar tana cewa Janar Ibrahim ya ce ana bukatar tallafi da shawarwarin Babban Hafsan Tsaron na Cadi don kawar da kalubalen da aka lura da shi.

Sai dai kuma sanarwar ba ta fadi ko wanne kalubale ne ake fuskanta a fagen yaki da ta’addancin ba.

Da yake mayar da martani, Janar Daoud ya ce a shirye yake ya bai wa MNJTF dukkan gudunmawar da take bukata don kawar da burbushin ’yan ta’adda daga tsibiran Tafkin Cadi da kewaye.

Ya kuma yi kira da a kara hada karfi da karfe don kawar da dukkan ’yan ta’adda daga yankin baki daya.

Sanarwar ta kuma ce Janar Ibrahim, wanda ke ziyarar tuntubar juna da kwamandojin rundunonin kasashen da suka kafa MNJTF, ya ziyarci hedkwatar rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da ke Maiduguri ranar Asabar, inda ya bukaci a kara hada hannu a tsakanin rundunonin biyu (MNJTF da OPHK).

Ya kuma jaddada bukatar musayar bayanan sirri nan take a tsakanin duka bangarorin don cimma manufar dawo da zaman lafiya a daukacin yankin da mayar da ’yan gudun hijira gidajensu.

Da yake mayar da martini, kwamandan OPHK, Manjo Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa Janar Ibrahim cewa a shirye rundunarsa take ta ba da dukkan hadin kan da ake bukata domin haka ta cimma ruwa.