✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yakin Najeriya a Laberiya ne silar rashin tsaro a teku’

Babban Daraktan Hukumar da ke kula da Sufurin Jiragen Ruwa tare da Lafiyar Teku ta Kasa (NIMASA), Bashir Yusuf Jamo ya ce matsalar tsaro a…

Babban Daraktan Hukumar da ke kula da Sufurin Jiragen Ruwa tare da Lafiyar Teku ta Kasa (NIMASA), Bashir Yusuf Jamo ya ce matsalar tsaro a tekun Najeriya na da alaka da yakin da kasar ta yi a Laberiya a lokacin mulkin soji.

Bashir Jamo ya ce a wannan lokacin Najeriya ta taimaka wa kawarta kasar Laberiya a yankin da ta yi da ‘yan tawaye, inda aka yi amfani da jiragen ruwan yaki na Nijeriya wadanda aka tanada domin ba da tsaro a sassan tekun Najeriya.

“A cikin shekarar 1994  kamar yadda ka sani Najeriya ita ce kan gaba wajen taimaka wa Laberiya a yakin da ta yi, yawancin jiragen ruwa da muke amfani da su wajen tsaron tekun kasa, sai ya zamana an aike da su zuwa yaki a Laberiya, domin su taimaka mata a matsayinta na kasa ‘yar uwarmu a yakin da take a wannan lokacin.

“Jiragen ruwa yadda aka gina su, suna da doka kamar yadda mota take, akwai adadin nisan zangon da za su yi su bukaci gyara ko juyen bakin mai kamar yadda ake yi wa mota.  Amma a wannan lokaci na yaki sai ya zamana babu damar yin haka, sai aka yi ta amfani da jiragen ba tare da an samu lokacin gyaran su kamar yadda doka ta sanya ba.

“Sai suka lalace aka kasa gyara su kuma ba a sami kudin da za a sayi sabbin da za su maye gurbinsu ba. Wannan shi ne tarihin yadda Najeriya ta fara shiga matsalar rashin tsaro a teku”, inji shi.

Ya ce shugabannin Najeriya da suka gabata sun gaji matsalar tun daga kan shugaba Obasanjo kuma kowannensu su ya fito da tsarin ko matakin gyara amma sai a lokacin gwamnatin Shugaba Buhari ne a ka cimma gagarumar nasara.

“Zuwan gwamnatin  Shugaba Muhammadu Buhari sai Ministan Sufuri Rotimi Amechi ya kawo wani kamfani da ake kira Deep Blue Sea Project, wato kamfani ne da ya ba mu damar da za mu shigo da manyan jiragen ruwa guda biyu wadanda a cikinsu akwai kanana guda 17, masu matukar gudu.

“Kananan jiragen ruwan idan an yi fashi a teku da su za a kai dauki. Yanzu haka manyan jiragen biyu sun iso kasar nan, sannan 15 a cikin kanan jiragen ruwan 17 sun zo saura biyu da za su zo.

“Sannan akwai jiragen sama da za su rika shawagi suna dauko hoton abubuwan  da ke faruwa. Idan an yi barna an gudu su jiragen za su iya bin su har doron kasa duk inda suka shiga.

“Wannan jiragen muna da manya guda biyu da za su zo cikin watan 8, wato watan Agusta na wannan shekarar, sannan akwai jirage masu saukar ungulu guda 3 da suma za su iso a watan Janairun shekara mai zuwa.

“Haka kuma muna da na’urar tauraron dan Adam wadda take kallon dukkan ruwan tekunmu. Za ta iya kallon abu daga nesa, ina daga ofishina ina ganin abun da ke faruwa sama da kilomita 200.

“Idan wani hari aka kai ina daga ofis zan gani, na’uarar za ta dauko mana hoto mu kuma dau matakin da za mu dauka cikin gaggawa”, inji Bashir Jamo.

Bashir Jamo ya shaida haka ne a zantawarsa da Aminiya a lokacin da ya gana da manema labarai a makon jiya.

Ya ce sun dauki matakin karfafa hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar tsaron tekun kasa wanda hakan ne ya sa aka yi nasarar kame mutum 17  da ake zargi da fashin teku, irinsa na farko cikin shekaru biyar.