✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yamuna Aminu Kani: Abar koyi a harkar kiwon lafiya

Dokta Yamuna Kani tana taimakon al’umma ta hanyar wayar da kai game da batutuwan kiwon lafiya

Lakabin da ake yi wa Dokta Yamuna Aminu Kani kaifi biyu ne: likita ce kuma dokta ta karatu — amma fa tana daf da zama farfesa — a fannin Lafiyar Mata a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutse.

Yanzu haka kuma, ita ce Shugabar Tsangayar Nazarin Magunguna da Kiwon Lafiya a jami’ar – ga shi kuma ita ta fara rike wannan mukami.

Shekara guda bayan ta fara aiki da Jami’ar, a 2016 ke nan, ta zama Jami’a Mai Kula da Jarrabawar Dalibai ta farko a Tsangayar.

A shekarar 2017 kuma ta zama Daraktar Kiwon Lafiya ta farko ta Jami’ar baki daya.

A lokacinta ne aka fara samun liktoci a asibitin Jami’ar suna aikin sa’o’i 24, aka kuma fara samun wutar lantarki ta sa’a 24 ta hanyar sarrafa hasken rana.

Tauraruwar tamu ta rike mukamai da dama a Jami’ar.

Aikin asibiti

Kafin ta fara aiki da Jami’ar Tarayya ta Dutse, Dokta Yamuna Aminu Kani ta yi aiki da Gwamnatin Jihar Jigawa.

Ita ce Shugabar Sashen Kula da Cututtukan Mata ta farko a Asibitin Kwararru na Rasheed Shekoni da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

A wannan matsayi, Dokta Yamuna Aminu Kani ta yi uwa, ta yi makarbiya wajen samar da kayan aiki na zamani don kula da lafiyar mata.

Haka kuma ita ce Shugabar dindindin ta farko ta Kwamitin Gudanarwa na Asibitin na Rasheed Shekoni.

Sannan ta shugabanci galibin kwamitocin da ake da su a asibitin, lamarin da ya ba ta damar kawo abubuwan ci gaba a sassan daban-daban.

Taimakon al’umma

Ba a cikin jami’a ko asibiti kadai Dokta Yamuna Aminu Kani ta takaita ayuukanta ba.

Tana kuma ayyukan taimakon al’umma ta hanyar shirye-shiryen rediyo da talabijin wadanda take amfani da su don wayar da kai game da batutuwan kiwon lafiya daban-daban.

Bayan haka, ta kan duba marasa lafiya kyauta, tana kuma shirya wa ma’ailatan lafiya tarurrukan bita a fadin Jihar Jigawa.