✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Abuja sun bijire wa umarnin Kotun Koli kan tsoffin kudi

Wannan na faruwa ne duk da kotu ta ba da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun na Naira

Bayanai sun nuna wasu ’yan kasuwa da dama sun daina karbar tsoffin takardun Naira a yankin Abuja.

Wannan na faruwa ne duk da umarnin da Kotun Koli da ya tsawaita amfani da tsoffin takardun Nairar na wucin-gadi zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu da muke ciki.

Da fari, bayan sauya fasalin takardun N200 da N500 da kuma N1,000, Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ayyana ranar 31 ga Janairu domin daina amfani da tsoffin takardun kudin da aka sauya.

Daga bisani CBN ya kara wa’adin zuwa 10 ga Fabrairu bayan kokawar da ’yan kasa suka yi.

Ana tsaka da haka ne gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da kara Kotun Koli inda suka nemi ta tsawaita wa’adin fiye da abin da CBN ya kayyade.

A kan haka ne kotun ta tsawaita amfani da tsoffin kudin zuwa 15 ga watan Fabrairu, ranar da za ta fara sauraron shari’ar.

A ranar Lahadi cewa, wasu ’yan kasuwa da masu motocin haya har ma da gidajen mai a yankin Abuja, na kin karbar wa tsoffin takardun na Naira.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito wani direban motar haya a Abuja, Mista Ndubuisi Ugwu, yana sanar da fasinjojinsa duk wanda zai shiga motarsa ya rike sabon kudi.

Saboda a cewarsa, “Na je sayen mai a gidan mai da tsoffin takardun Naira, amma suka ki karba.”

Haka ita Amina Shuaibu, mai sayar da tumatiri a Kasuwar Karu, ta ce tun ranar 11 Fabrairu ta daina karbar tsoffin takardun Naira.

“Kodayake na ji wai kotu ta ba da umarni a ci gaba da amfani da tsoffin kudin, amma mutane na kin karbar su a kasuwa shi ya sa ni ma na daina karba.

“Na kuma ji cewa bakuna ma sun dai a karba amma ba ni da tabbacin ko gaskiya ne.

“Akwai rudani batun, mafita shi ne a daina karba,” in ji ta.

Wata daliba mai suna Vivian Anibe, ta ce ta yi amfani tsohuwar N1,000 da ta rage mata wajen sayen abubuwan da ba ta yi niya ba.

“Na fito domin in sayi burodi amma hakan bai samu ba saboda mutane da dama sun daina karbar tsoffin takardun Naira.

“Da na jaraba zuwa wani shago na ga suna karba dole, na sayi abin da ban yi niyya ba. Amma na ji dadi tunda na samu kashe kudin” in ji Vivian.

(NAN)