✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Arewa a Kudu ku rika sa ’ya’yanku a makaranta — Kwankwaso

Ba yaro ilimi na da matukar muhimmancin a rayuwa da ta zaman Kudu.

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya shawarci ’yan Arewa mazauna Kudu su bai wa ’ya’yansu ilimin zamani.

Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne a makon jiya a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, lokacin da ya je godiyar ban-gajiya da gode wa wakilai masu zaben ’yan takara a jihar.

Ya ba su shawarwari kan zamantakewa inda ya ce, “Ina ba ku shawara ku ’yan uwana ’yan Arewa mazaunan wannan jiha ku rika kai ’ya’yanku makaranta, ba yaro ilimi na da matukar muhimmancin a rayuwa da ta zaman Kudu.”

Dan takarar na Jam’iyyar NNPP ya shawarci magoya bayan jam’iyyarsa su yi rajistar katin zabe kafin a rufe yin rajistar domin da katin zaben da suka yi ne za su nuna masa cikakkiyar kauna da goyon baya a zabe.

Kwankwaso ya kara da cewa, babu wani dan Najeriya da zai zauna yana ji yana gani an ki a gyara matsalolin da suka addabi kasa da al’ummarta.

Ta hanyar zaben NNPP idan ta kafa gwamnati ce kadai za ta iya magance “matsalar da wadansu masu ikirarin canji suka gaza gyarawa shi ya sa muka hadu da matsaloli, hakan ya sa muka ba su wuri muka kafa tamu jam’iyyar,” inji shi.