Daily Trust Aminiya - ’Yan awaren Biyafara sun kai wa Fulani hari a Imo
Subscribe

Wasu ’yan awaren Biyafara

’Yan awaren Biyafara sun kai wa Fulani hari a Imo

A yinin ranar Talatar da ta gabata ce ’yan awaren Biyafara suka kai wa Fulani da ke kauyen Orji hari, lamarin da ya jikkatar da mutum biyu da a halin yanzu ana jinyarsu a Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC Owerri.

Aminiya ta samu tabbaci a kan harin wanda aka kashe wa makiyaya shanu 15 ta bakin Honarabul Sani Ahmad, shugaban Al’ummar Arewa mazauna jihar Imo.

Honarabul Ahmad ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, “ka ji mutanen nan abinda suka yi ko? Sun sake kai wa Fulani hari, sun kashe mutum daya sannan biyu na kwance a Babban Asibitin Tarayya wato FMC inda suke karbar magani.

“Sun kashe musu shanu 15 sannan sukan zakulo duk inda yan Arewa yake a jihar Imo su tambaye su ko su na da takardar Biza ta shigowa kasar Biyafara.

“Idan babu sai su hau su da duka da sara da Adda wani zubi kuma har da harbi da Bindiga suna cewa nan fa ba Najeriya bace ku sani kunzo kasar Biyafara ce.”

Ya zuwa yanzu dai jimillar ’yan Arewa 12 ke nan masu fafutikar kafa yankin Biyarafa da aka fi sani da IPOB suka kashe baya ga salwantar musu da dukiyoyinsu.

Wakilinmu ya tuntubi wasu daga cikin mazauna jihar Imo ko sun fara sayen kayayyaki da takardun kudin Biyafara, sai da sun ce, “a’a ba’a kai ga wannan gabar ba.”

Ana iya tuna cewa, shekara 20 da ta gabata, a kan yi cinikayya da takardun kudi na Biyafara a garin Aba na Jihar Abiya.

More Stories