✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan banga da mafarauta sun kashe ’yan bindiga 47 a Neja

Sun yi wa maboyar ’yan bindigar kwanton bauna suka yi ta musu ruwan wuta.

’Yan banga da mafarauta sun kashe ’yan bindiga akalla 47 a wani kwanton bauna da suka yi wa sansanin ’yan bindiga a Jihar Neja.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa ’yan bindigar da suka addabi yankunan Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar sun sheka lahira ne bayan ’yan banga da mafarautan sun shammace su a maboyarsu da ke wani yani a tsakanin Kananan Hukumomin Rafi da Shiroro inda suka yi sansanoni.

“Ina tabbatar muku cewa ’yan bindigar sun kwashi kashinsu a hannu. Mafarauta sun kashe akalla 47 a harin,” inji jami’in da ya nemi kafar ta boye sunansa.

Ta ambato dan sandan, wanda jami’in tattara bayanai ne, yana cewa baya ga ’yan bindigar da aka karkashe su 47, akwai wasu da dama da suka tsere da raunin harbi a jikinsu.

Ba a bayyana sunan yankin ba saboda dalilan tsaro, amma inda abin ya faru na kusa da wani rafi ne a tsakanin kananan hukumomin da aka amabata.

PRNigeria ta ruwaito wata majiya na cewa gamayyar ’yan banga da mafarauta sun yi wa ’yan bindigar ba-zata a sansanonin nasu ne a ranar Laraba, suka yi ta yi musu luguden wuta babu kakkautawa.

Babu tabbacin ko ’yan bangar da mafarautan da suka yi wa ’yan bindigar kwanton bauna na daga cikin gamayyar ’yan san kai na (NSVC) da Gwamantin Jihar Neja da hadin gwiwar Rundunar ’Yan Sandan Jihar suka kaddamar a watannin baya.

A lokacin da yake kaddamar da su, Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce mutanen jihar ba za su zura ido ’yan bindiga su rika yi musu diban karan mahaukaciya ba.

“’Yan bindiga so suke su tilasta mu sauya yadda muke rayuwa a Jihar Neja amma ba za mu zura musu ido ba,” inji shi.

“Sun hana ’ya’yanmu zuwa makaranta, sun hana mu bin hanyoyi, sun hana manoma zuwa gona, suna dai so su hana mu yin komai.

“Amma ba za mu girgiza ba, ba kuma za mu bar hakan ta faru ba; za mu ci gaba da rayuwa yadda muka saba,” inji shi a lokacin da yake kaddamar da NSVC a watan Yuni.