✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan banga sun fille kan dan bindiga, sun cafke wasu 6 a Katsina

’Yan banga sun fille kan gawurtaccen dan bindiga da ya addabi hanyar Jibiya zuwa Batsari

’Yan banga sun yi nasarar fille kan wani gawurtaccen dan bindiga tare da kama wasu shida da ransu a Jihar Katsina.

’Yan bindigar sun kwashi kashinsu a hannun ’yan bangar ne a wani harin bata-garin da ’yan banga suka dakile a Karamar Hukumar Batsari ta jihar.

Alkaluman da muka samu na ’yan bindigar da aka kashe sun sha bamban, amma majiyoyinmu sun tabbatar cewa an kama ’yan bindiga akalla shida.

Wasu majiyoyi a Batsari sun ce ’yan bindiga tara aka kashe, wasu kuma na cewa daya shida ne, a yayin da wasu suka ce mutum daya ne.

Amma wani bidiyo da ka yada bayan artabu ya nuna wata gawa da aka file wa kai tare da sare kafarta daya.

Akwai wani bidiyo kuma da ya nuna mutanen garin suna murna kan nasarar da ’yan bangar suka samu, tare da nuna kai da kafar dan bindigar da aka kashe.

Wata majiya a Batsari ta shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun kai hari garin ne da misalin karfe 4:30 na yamma ranar Lahadi suna harbi, inda suka kashe mutum daya suka kuma sami wani da harbi.

Bayan nan ne rundunar hadin gwiwar ’yan banga da Civilian JTF da jami’an tsaro suka kawo dauki, suka kashe daya daga cikinsu tare da tsare wasu da dama.

Wata majiyar ta ce ’yan bindigar da aka kashe sun kai mutum tara, an kuma tsare wasu biyar.

Ya bayyana cewa gawar da aka yada wa mutane ta wani gawurtaccen dan bindiga ne da ya addabi matafiya a hanyar Batsari zuwa Jibiya.

“Ya yi kaurin suna a yankin shi ya sa aka fille kansa aka kawo gawarsa domin kowa ya shaida; amma sauran gawarwakin an bar su a cikin daji,” in ji majiyar.

Ta kara da cewa ’yan banga sun kwace babura kimanin tara daga hannun ’yan bindigar.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, amma ya ce bai samu rahoto daga DPO na yankin ba.

SP Gambo Isah ya yi alkawarin cewa zai tuntubi wakilinmu idan ya sami bayani, amma har zuwa lokacin da aka kammala rubuta wannan labari ba mu ji daga gare shi ba.