✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga daga Zamfara da Katsina sun fara kai hari Kano

’Yan bindigar sun fara kai hari suna garkuwa da mutane a Rogo.

Hare-haren da sojoji suke kai wa ’yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara sun tilasta musu tserewa zuwa Jihar Kano da ma wasu jihohin. 

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Rogo da Karaye a Majaliar Wakilai, Haruna Isah Dederi, ya ce a kwanakin baya ’yan bindiga sun kai hare-hare gami da garkuwa da mutane garuwa bakwai a Karamar Hukumar Rogo ta Jihar Kano.

Ya ce garuruwan ’yan bindiga suk yi garkuwa da mutane a yankin sun hada da garin Jajaye, Zarewa, Ruwan Bago, Bari, Falgore, Dutsen Ban da Hawan-Gwamna (Fulatan).

“Idan ba a gaggauta daukar matakai ba na hana yaduwar ’yan bindigar a Karamar Hukumar Rogo da wasu kananan hukumomin Jihar Kano musamman wadanda ke kan iyaka, matsalar na iya yaduwa zuwa wasu kananan hukumomi tare da gurgunta amincin da ake da shi a jihar Kani,” inji dan Honorabul Dederi.

Ya yi kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara tsanantawa wajen ragargazar da take wa ’yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina ta hanyar fadada matakan zuwa wasu wurare.

A cewarsa, yin hakan na da muhimmanci a sauran yankunan da matslar ta shafa domin gudanar da hare-haren a lokaci guda zai hana bata-garin samun sukunin tserewa zuwa wasu wuraren.