✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga: Daliban Sakandire sun tsere bayan an kashe mutum 13 a Zamfara

Da misalin karfe 1.00 na tsakar rana ’yan bindigar suka yi wa yankin dirar mikiya.

Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai yankin Damaga a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Aminiya ta samu cewa ’yan bindigar bila adadin sun kai harin ne haye a kan babura sannan suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi gabanin su yi awon gaba da wasu shanu da suka fita kiwo.

Aukuwar wannan harin ya sanya nan take wasu dalibai suka arce daga makarantarsu ta sakandiren Damaga yayin da suka ankara da lamarin da ke wakana domin tseratar da rayukansu ko abin da ka iya zuwa ya dawo.

Wani mazaunin yankin da ya zanta da wakilinmu mai suna Musa Damaga, ya ce ’yan bindigar sun yi wa yankin nasu dirar mikiya da misali karfe 1.00 na tsakar rana.

A cewarsa, “daliban wata makarantar sakandiren jeka ka dawo da ke tsaka da daukan darasi suna hangen ’yan bindigar suka watsar da karatunsu suka ranta a na kare domin neman tsira.”

“A halin yanzu muna ci gaba da lalubo gawawwakin mutanen da suka mutu kuma mun kammala shirye-shiryen yi musu jana’iza,” a cewar Musa.

Yayin da aka tuntubi jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar SP Muhammad Shehu, kai tsaye ya ce a bashi lokaci zai waiwayi wakilinmu.

Jihar Zamfara tana daya daga cikin jihohin da ’yan bindiga suka uzzura wa al’ummominsu, inda a baya-bayan nan Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin tura karin dakarun soji dubu shida domin rubanya kokarin da hukumomin tsake ke yi na magance matsalolin tsaro a jihar.