✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga: Gwamnatin Kaduna ta ziyarci kauyukan hanyar Abuja

Hadin guiwar Jami'an tsaro da gwamnatin Kaduna sun ziyarci wasu kauyuka da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Gwamnatin Jihar Kaduna tare da guiwar jami’an tsaro sun ziyarci kauyukan da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja don jajanta musu game da ayyukan ’yan bindiga.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan da Kwamandan Rundunar Operation Thunder Strike, Kanar Ibrahim Gambari, na daga cikin wadanda suka ziyarci kauyukan.

“Kamar yadda kuke gani jami’an tsaro na daukar matakan sirri don kawo karshen ayyukan ’yan bindiga, saboda haka yana da kyau ku ba su hadin kai”, a cewar Aruwan.

Ya kara tabbatar wa da mazauna yankin cewa gwamnati ta damu matuka da irin halin da suke ciki na ayyukan ’yan bindiga, kuma ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi kokarin magance matsalar cikin dan lokaci.

Ayyukan ’yan bindiga da yin garkuwa da mutane, al’amari ne da ya addabi mazauna kauyukan da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A wasu jihohin Arewa musamman Katsina, Zamfara, Sakkwato, Neja, Nasarawa da Kebbi, yin garkuwa da mutane na baranaza ga rayuwar mutane, wanda kume ke tilasta wasu yin kaura zuwa wasu yankunan.