✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga: Jami’an tsaro sun fara sintiri a dazukan Kano

An tabbatar wa da al’ummar Jihar Kano aminci kan rayukansu da dukiyoyinsu.

Jami’an Tsaro da suka hada da dakarun soji, ’yan sanda da na hukumar Civil Defence da ma mafarauta, sun fara aikin hadin gwiwa na gudanar da sintiri da tsefe Dajin Falgore da sauran dazuka a Jihar Kano.

Wannan na zuwa ne bayan mako guda da Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi gargadi tare da bayyana fargaba game da shigowar ’yan bindiga cikin dazukan Jihar.

Cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Al’umma na Rundunar Sojin Kasa, Birgediya-Janar Mohammed Yerima ya fitar a ranar Laraba, ya ce sojojin runduna ta 1 na aiki tare da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a Jihar Kano.

A cewarsa, manufar wannan aikin sintiri da tsefe dazukan da suka fara gudanarwa ita ce tabbatar da cewa ’yan daban daji, masu garkuwa da mutane da sauran ’yan ta’adda ba su kwararo ba daga jihohin da ke makwabtaka da Kano.

“Saboda haka, muna mai tabbatar wa da al’ummar Jihar Kano aminci kan rayukansu da dukiyoyinsu.

“Muna kuma bukatar da su ci gaba da kai rahoton duk wani motsi na wasu mutanen da suka gani wanda ba su yarda da su ba zuwa ga hukumomin tsaro mafi kusa domin daukar matakin gaggawa.

“Rundunar sojin kasan tare da hadin gwiwar dukkanin masu ruwa da tsaki sun kudiri aniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma a Jihar Kano da sauran jihohin da ke kewayenta,” a cewar Yerima.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Gwamna Ganduje ya bayyana fargabar cewa ’yan bindiga sun fara dandazo a wasu dazuka na jihar.