✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘’Yan bindiga na hada baki da sojoji’

Wanda ya tsallake rijiya da baya ya fallasa abin da ya gani.

Wani direba da ’yan bindiga suka tsare motarsa kuma ya ruga cikin daji a tsakanin Kaduna da Zariya ya yi zargin cewa akwai hadin baki a tsakanin masu satar mutane da sojoji da sauran jami’an tsaro.

Direban, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa Aminiya haka ne a lokacin da take gudanar da bincike a kan hare-haren ’yan bindiga a yankin Masarautar Zazzau.

Ya ce, “Bayan sun tsare mu sai na fita da gudu na yi cikin daji, ina cikin gudu mutanen suna bi na sai na hango motar sojoji.

“Sai na dan labe; sai sojojin suka ce da ’yan bindigar ‘Su wane ne?’ Sai suka ce su ne su wane.

“Sai kawai ’yan bindigar suka koma da baya. Hakan ne sanadin da ni ma na tsira,” inji shi.

Ya ce in babu hadin baki, yaya aka yi daga fadin sunansu sai sojojin suka ci gaba da harkokinsu, su kuma suka koma inda suka fito?

An dai jima ana zargin hadin baki a tsakanin ’yan bindiga da jami’an tsaro, amma hukimomin tsaro sun sha musawa tare da shan alwashin hukunta duk jam’insu da aka samu da hannu a ayyukan ’yan bindiga.

Kokarin jin ta-bakin Kakakin Rundunar Soji ta Daya da ke Kaduna, Kanar Ezindu Idima, ya ci tura domin layin wayarsa bai shiga ba.

Amma wata majiya a Rundunar ta shaida wa Aminiya cewa bata-gari na iya saka kayan sojoji su aikata ba daidai ba, don haka sai an kama irinsu za a tabbatar da ko sojojin gaske ne ko na bogi.

Musulmi sun koma ga Allah

Yawaitar hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa a sassan Zariya suna sace mutane, a baya-bayan nan ta sa wadansu malaman Musulunci a yankin gudanar da Salatul Haja tare da Alkunutu domin rokon Allah Ya kawo dauki kan abin da yake faruwa.

Malam Tanimu Abubakar Mai Rawani, daya daga cikin wadanda suka shirya sallolin, ya ce yin wannan ibada ya zama wajibi a irin wannan lokaci saboda Sunnah ce ta Manzon Allah (SAW) duk lokacin da abu yake faruwa mutane su kaskantar da kai su koma bayan gari domin addu’o’i da neman Allah Ya kawo dauki.

Ya ce mutanen Zariya suna cikin tsaka-mai-wuya kuma ba sa iya barci, saboda matsalar tsaro na neman fin karfin gwamanti.

Malam Tanimu Mai Rawani, ya kuma ce suna sa ran da wannan insha Allah ayyukan ta’adanci sun zo karshe a Najeriya.

Koyarwar addini

Da yake bayani bayan kammala addu’o’in, Sheikh Malam Habibu Usman ya ce ta’adanci irin na masu garkuwa da mutane ya saba wa koyarwar addini.

Ya kuma ce wajibi ne gwamnati ta yi duk mai yiwuwa don kawo karshen wannan matsala.

Shi kuwa Garkuwan Makarantar Zazzau, Alhaji Shamsuddin Aliyu, ya ce lokaci ya yi da za a bar mutane su dauki matakin kare kansu, saboda a zahiri gwamnati ta gaza.

Ya ce dole jama’a su koma ga Allah kowa ya gyara zuciyarsa; idan aka yi haka ana sa ran za a samu mafita.

Garkuwan Makarantar Zazzau ya ce jarrabawa biyu jama’a ke fama da ita, akwai ta gwamnati da ta masu garkuwa da mutane.

Ya ce korar ma’aikata da gwamnati ke yi ba gaira ba dalili yana sabbaba karuwar marasa aikin yi.

Sai ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai su samar wa matasa aikin yi domin rage zaman kashe wando da ake fama da shi.