✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga na haurowa Najeriya daga Mali —Makinde

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, ya bayyana cewa ’yan bindiga na ribatar kusancin da jiharsa ke da shi da wasu iyakokin Najeriya su ketaro…

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, ya bayyana cewa ’yan bindiga na ribatar kusancin da jiharsa ke da shi da wasu iyakokin Najeriya su ketaro cikin kasar nan.

Makinde ya yi wannan furuci ne yayin da ya kai ziyara Masarautar Okere ta Saki, inda ya gana sarakunan gargajiya.

Sai dai ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar dakile hare-haren ’yan bindiga da taimakon sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

A yayin ziyararsa, Gwamna Makinde ya ba su tabbacin cewa gwamantinsa za ta ci gaba da fadi-tashin ganin ta dakile ayyukan ’yan bindiga a jihar.

A cewarsa, Masarautar Saki na kusa da wasu iyakokin Najeriya da wasu kasashen, wanda ta nan ne ’yan bindiga daga Mali ke haurowa cikin Najeriya.

Kazalika, gwamnan ya jinjina wa masu sarautar gargajiyar game da irin gudunmawar da suke ba wa gwamnatinsa domin ci gaban al’umma.