✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga na samun taimako daga kasashen waje —NSCDC

“Da gaske suke; suna da masu daukar nauyinsu daga kasashen duniya...”

Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSDC) Ahmed Audi, ya ce ’yan binidga na da masu taimaka musu daga kasashen waje.

Ya fadi haka ne a yayin taron horas da kwamandojin NSCDC na jihohi a Abuja, ranar Laraba, inda ya ce Najeriya na fama da yakin wanda ke bukatar hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Ya ce ’yan binidga, “Da gaske suke; suna da masu daukar nauyinsu daga kasashen duniya, don haka ya kamata mu hadu.”

“Yadda abubuwa ke faruwa a kasar, muna fuskantar mummunan rikici wanda nake ganin a tarihin Najeriya, shi ne rikici na farko da zai ba mu babbar matsala.

“Mun sha fuskantar irin wannan yakin amma sai wannan lokaci muke ganin hakikanin bayyanarsa.

“Yakin kuma abu ne da ke bukatar hada karfi da karfe magance ta gaba daya,” inji Shugaban na NSCDC.

Audi ya yi kira ga hukumomin tsaro da su guji sa-in-sa a tsakanainsu, yana mai jaddada cewa ana bukatar hadin gwiwa don cin nasarar yaki da ’yan ta’adda.