✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga na yi wa matan aure fyade a kauyukan da suka ‘kwace’ a Taraba

Mazauna yankin dai sun ce tilas sun mika wuya saboda yanke kaunar samun dauki daga gwamnati

’Yan bindiga sun kwace kauyuka da dama a Kananan Hukumomin Gassol da Karim Lamido da ke Jihar Taraba.

Aminiya ta gano cewa kauyen da harin ’yan bindigar ya fi muni a cikinsa shi ne Kambari, wanda ke Karamar Hukumar Karim Lamido.

Garin dai na bakin Kogin Binuwai, kuma ba shi da nisa da iyakar Jihar da Filato.

Shi da sauran garuruwan da ke da makwabtaka da shi suna da manyan dazuka, sannan ba su da kyawawan hanyoyi, lamarin da ya sa suka zama mafakar bata-garin.

Rahotanni sun kuma ce tsananta hare-haren ’yan bindigar ya tilasta wa ’yan sanda da ’yan sa-kai barin wuraren aikinsu a yankin.

Kazalika, wasu majiyoyi a yankin sun ce maharan na yi wa matan aure da ’yan mata fyade.

Mazauna yankin dai sun ce tilas sun riga suka mika wuya saboda yanke kaunar samun dauki daga gwamnati.

Bugu da kari, wasu kauyukan ma da ke yankin na fuskantar barazana daga ’yan ta’addan, lamarin da ya tilasta wa mazauna wasu kauyuka shida a Kananan Hukumomin yin hijira.

Kauyukan sun hada da Gwammo da Wurno da Tungan Kaya da Gidan Kawoyel da kuma Ali Kwala.

Kazalika, su ma garuruwan WuroJam da Karar da Shika da Amar da Zip da WuruJam da Illela da kuma Maigemu su ma yanzu suna cikin babbar barazana.

’Yan ta’addan dai kan yi kai da kawowarsu yadda suke so da makamansu tsirara, ba dare ba rana.

Su kan kuma sace duk wanda suke so a duka lokacin da suka ga dama, ciki har da matan aure.

A wasu daga cikin kauyukan, sun debi kananan yara inda suke amfani da su wajen tattara bayanai, musamman a kan gidajen masu hannu da shuni.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan Sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya ce har yanzu rundunarsu ba ta samu rahotannin hare-haren ba.

A cewarsa, Ofishin Baturen ’Yan Sandan yankin bai aika musu da kowane irin rahoto a kan kwace kowane kauye a yankin ba.

“Idan gaskiya ne ’yan ta’adda sun kwace kauyen Kambari ko ma kowane kauye, me ya sa mutanen yankin ba su sanar da ’yan sanda ba?” inji Kakakin.