✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga: Rundunar Sojin Kasa ta gargadi Sheikh Gumi kan lafuzansa

An gargardi Shehin Malamin da ya kiyaye lafuzansa sannan kuma ya yi wa harshensa linzami.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta bayyana damuwa a kan wasu kalamai da ake jingina wa fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na cewa sojojin da suka juya wa addinin Muslunci baya ne ke kai wa ’yan bindiga hare-hare.

An nado Sheikh Gumi a cikin wani bidiyo yana cewa galibin sojojin da ke faman kai wa ’yan bindiga hare-hare ba Musulmai ba ne.

Sai dai a yayin da take mayar da martani dangane da lamarin, rundunar sojin ta gargardi shehin malamin da ya kiyaye lafuzansa sannan ya yi wa harshensa linzami musamman a kan kalaman da yake alakanta wa da rundunar.

Rundunar ta bakin kakakinta, Birgediya Mohammed Yerima, ta ce ba akidarta ba ce nuna bangarancin addini ko kabila wajen tura dakaru su kawar da bata-gari daga cikin al’umma.

Sanarwar da ta fitar ta ce, “Mun ankara da wani bidiyo da ke yawo na nado babban malamin Islama, Sheikh Ahmed Gumi yana zargin sojojin da ba Musulmai ba da kai wa ’yan bindiga hare-hare.

“A cikin bidiyon, babban malamin yana cewa galibin sojojin da ke kai wa ’yan bindiga hare-hare ba Musulmai ba ne, har yana cewa ’yan bindigar su sani cewa a cikin sojoji akwai Musulmai akwai wadanda ba Musulmai ba.

“Duk da cewar Rundunar Sojin Kasa ba ta muradin sa-in-sa ta shiga da Sheikh Ahmad Gumi, amma tana jaddada cewa kasancewarta hukuma a Najeriya, ba ta la’akari da bangaranci addini ko kabila yayin tura dakarunta aiki.

“Saboda haka, Sheikh Ahmed Gumi da sauran masu sha’awar bayyana ra’ayi, su yi taka-tsantsan don kada su zubar da mutunci ko martabar Rundunar Sojin a matsayinta na babbar Hukuma kuma abin dogaro a kasar.

“Rundunar sojin kasan za ta ci gaba da kasancewa abin alfahari ga Najeriya kuma ba za ta gushe ba wajen ci gaba da kare martabar wannan kasa; furta lafuzan da zai zubar da mutuncin rundunar na iya janyo tsana da tsangwama a tsakanin ’yan kasar.

“Bugu da kari, galibin ayyukan da rundunar take gudanarwa tana aiwatar da su ne a bisa tafarki na tsananta kiyaye duk wata doka da ka’idoji tare da tabbatar da daraja da kiyaye ’yancin rayuwar al’umma ba tare da nuna wata wariya ba.

“Saboda haka a yanzu akwai babbar damuwa dangane da furucin bayyana ra’ayi da wani jagoran al’umma ya yi da gangan domin zubar da mutuncin Rundunar Sojin Kasa.

“Rundunar tana amfani da wannan dama ta shawarci duk wasu jagororin al’umma masu sha’awa bayyana ra’ayi da su rika furta kalamai masu taushi yayin bayyana ra’ayoyinsu tare da la’akari da halin da kasar ta tsinci kanta na matsalolin tsaro.”