✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga: Sojoji sun kubutar da mutum 10 a Zamfara

Sojoji sun ragargaji ’yan ta’addar sannan suka kuma cafke wasu

Dakarun rundunar soji ta Operation Hadarin Daji mai yaki da masu garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci sun ceto mutum 10 da suka fada komar masu garkuwa da mutane a kauyen Yenyewa da ke Jihar Zamfara.

Jami’in yada labaran rundunar, Manjo-Janar John Enenche, ya bayyana haka a ranar Talata a Abuja.

Enenche, ya ce bayan samun rahoton ’yan ta’addar na cin karansu babu babbakar a yankin ne aka tura sojoji suka mamaye su a ranar Lahadi 20, ga watan Disambar 2020.

“Yanzu haka mutanen da aka yi garkuwar da su tuni sun sadu da Iyalansu,” inji shi.

Enenche, ya ce rundunar Operation Whirl Stroke ta kashe dan bindiga daya ta kuma cafke wasu biyu a Jihar Binwai a ranar Litinin.

“An kwato bindiga kirar AK-47 da harsasai samfurin 7.62mm,” inji shi.

Ya ce ’yan bindigar na da alaka da kisan wani lauya a Makurdi  da matarsa.