✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun aike wa mutanen Shinkafi wasikar hari

’Yan bindigar suna kai daidaikun hare-hare a yankin.

’Yan bindiga sun aike da wasika cewa za su kai hari a Karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara.

Kafar yada labarai ta RFI Hausa ta ruwaito daya daga cikin dattawan garin da ke zaune Abuja, Dotkar Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, yana cewa wasikar ta kada musu hanta, sannan ya roki gwamnatin ta kai wa garin dauki.

An kama babur 202 na ’yan bindiga a Katsina

Takaddama Kan Yi Wa Malaman Jihar Kano Gwajin Kwakwalwa

“Muna kira ga gwamnatin tarayya ta yi kokari ta taimaka wa bayin Allah da ke cikin garin Shinkafi da kewaye domin wannan wasika ta tayar mana da hankali,” inji Dokta Shinkafi.

Ya kuma bayyana cewa, sun samu rahotannin da ke tabbatar cewa, an yi harbe-harbe a garin, mako uku bayan toshe layukan sadarwa a Jihar, inda sojoji ke ragargazar bata-garin.

Wani daga cikin masu bibiyar Aminiya ta Facebook, ya aiko mana da sako cewa ’yan bindigar sun aika sako cewa a ranar Juma’a za su kai harin.

A cewarsa, sau uku a cikin mako gudan ’yan bindigar suka kai hare-hare a garin “Suka kashe mutane da dama jiya da yamma da kuma cikin dare, wadanda suka jikkata kuma an kai su Babban Asibitin Garin Shinkafi.

“Sannan suna kai hari a kan hanyar Kauran Namoda zuwa Shinkafi.

“Ya kamata gwamnati ta je har maboyar ’yan ta’addar nan ta kawar da su gabat dan”, inji shi.

A halin yanzu dai babu wata hanya da za a iya tabbatar da ikirarin nasa, ko sanin halin da ake ciki a garin game da harin da ake barazana.

Mun so mu ji daga bakin mazauna garin, amma babu wata hanya ta tuntunbar su, saboda rufe layin sadarwa a fadin Jihar Zamfara